
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga Gwamna Siminalayi Fubara da shugabannin siyasa da mabiyansu a Jihar Ribas su ƙaurace wa fitina tare da kiyaye doka.
Hakan na zuwa ne sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a jihar wanda ya haddasa tashin-tashina da tashe-tashen bama-bamai a yankunan manyan ofisoshin ƙananan hukumomin jihar saboda ƙin amincewa da sakamakon zaɓen daga wani ɓangare na al’ummar jihar.
Shugaba Tinubu ya umarci jami’an ƴan sanda su gaggauta dawo da zaman lafiya da kiyaye doka da oda.
Ya nuna muhimmancin kula da kiyaye doka da kuma kare kadarorin gwamnati da aka gina da dukiyar al’umma.
Ya ƙara da cewa, shari’a za ta yi hukunci game da sakamakon zaɓen matuƙar aka samu rashin amincewa daga wani ɓangare, don haka babu buƙatar tayar da rikici.
