Da Ɗumi-ɗuminsa: Gwamna Sule ya sauke kwamishinoninsa

Labarin da ya shigo wa MANHAJA yanzu-yanzu daga jihar Nasarawa, ya nuna Gwamnan Jihar, Engr. Abdullahi A.Sule, ya rushe ‘yan majalisarsa.

Gwamnan da kansa ya ba da sanarwar sauke ‘yan majalisar a yau Litinin bayan wani taro na masu ruwa da tsaki a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Lafia.

Wannan mataki ya shafi har da masu bai wa Gwamna shawara da sauransu.

Gwamna Sule ya yaba wa kwamishinonin da hadiman da ya sauke bisa gudunmawarsu da suka bayar wajen cigaban gwamnatinsa da ma jihar baki ɗaya.