Ba mu da wani shirin soma yajin aiki yau Talata, cewar ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce, ba ta da wani shiri na soma yajin aiki aiki a yau Talata, kamar yadda ɗaya daga cikin shugabannin ASUU na ƙasa ya shaida wa manema labarai.

Dr. Dele Ashiru, wanda kuma shi ne shugaban ASUU reshen Jami’ar Legas, ya shaida wa manema labarai a jiya Litinin cewa, ba haka kawai ASUU ke shiga yajin aiki ba face sai da cika wasu sharuɗɗanta.

Ashiru ya ce lallai ne ƙungiyar ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin zuwa Talata, 31 ga Agustan 2021, a kan ta biya mata wasu buƙatunta.

Yana mai cewa, “Da a ce gwamnati ba ta cimma buƙatunmu ba a tsakanin wa’adin da muka ba ta, hakan ba yana nufin a wannan rana za mu soma yajin aiki ba.

“Dalili kuwa shi ne cewa, ASUU ba ta mutum guda ba ce, idan ba a cimma buƙata ba shugabannin ƙungiyar na ƙasa za su kira taro su tattauna batun. A wannan wuri ne za a yanke shawarar mataki na gaba da ya dace a ɗauka.

Jami’in ya ƙara da cewa, “Buƙatunmu a wajen gwamnati guda uku ne kacal; so muke gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da muka sabunta da ita, da batun alawus ɗinmu, sai kuma biyan Naira bilyan N40 don farɗo da ingancin jami’o’i.”