Kotu ta yi fatali da buƙatar Malami ta neman janye dokar haramcin kama Igboho

Alƙali Ladiran Akintola na Babbar Kotun Jihar Oyo, ya ƙi amincewa da buƙatar Babban Lauyan Nijeriya (AGF) Abubakar Malami, ta neman kotu ta janye dokar haramta kama Chief Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho da ta shata, wadda ta haramta wa Malami da sauran hukumomin tsaro damƙe Igboho.

Kotun ta ƙi amincewa da buƙatar Malami ne yayin zamanta a jiya Litinin bayan da Lauyoyin Malami suka ɗaga batun a gabanta.

Lauyoyin sun buƙaci kotun da ta janye dokar haramcin kama Igboho saboda a cewarsu, wannan abu ne da bai kamata ya zarce kwanaki bakwai ba.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 4 ga Agusta kotu ta sanya wannan doka wadda ta hana Babban Lauyan Nijeriya Malami da sauran hukumomin tsaro zarafin kamo Igboho ko yi masa wata barazana.

Alƙalin kotun ya dake kan matsayarsa cewa janye dokar haramta kama Igboho ɗin ka iya haifar da a kashe Igboho tun kafin a kai ga yanke masa hukunci.

Don haka ya tsawaita wa’adin dokar har zuwa ranar da za a ci gaba da shari’ar.

Daga bisani, lauyan hukumar tsaro ta DSS, Mr. T. A. Nurudeen, ya buƙaci kotun da ta ɗage ci gaba da shari’ar domin ba shi damar tattara bayanan da za su daƙile bayanan da lauyan Igboho, Chief Yomi Alliyu ya shigar kan rashin yarda da ƙorafin da Malami ya yi na cewa kotun ba ta da hurumin sauraron wannan shari’ar.

A halin da ake ci dai kotun, ta ɗage ci gaba da sauraron wannan shari’ar ya zuwa 7 ga Satumba n 2021.