Uwargidan Ganduje za ta fito takara a Jigawa

Daga ABUBAKAR M. TAHEER a Haɗejia

Cikin ’yan kwanakin nan labarin takarar Uwargidan Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, wato Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje, yana daɗa jan hankulan al’ummar jihohin Kano da Jigawa.

Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje, wacce ta ke ’yar asalin garin Malam Madori da ke Jihar Jigawa ce, ta kasance macen da masu sharshi kan al’amuran yau da kullum kan kalli lamarinta a matsayin akwai lauje cikin naɗi.

Cikin kwanakin baya an jiyo amon zugar wasu ’yan jam’iyyar APC na cewa, sun bar jam’iyyar ta APC sakamakon kallon tafiyar hawainiya da jam’iyyar ta ke yi.

Al’ummar yankin na Malam Madori da Kaugama suna kallon ɗan Majalissar Wakilai mai wakiltar yankin, Hon. Makki Yallema, a matsayin wanda ya kasa assasa musu komai a tsawon shekarun da ya ke wakiltar su.

Duk da Farfesa Hafsat Ganduje ba ta fito ƙarara ta bayyana aniyarta a fili na neman kujerar ba a zaɓe mai zuwa na 2023, amma alamu na nuna cewa akwai wannan ƙuduri a ƙasa inda mutanen yankin suka sha alwashin zaɓarta.

Daga cikin dalilan masu sharshi kan lamuran siyasa akwai cewa tana kawowa yankin cigaba wanda ’yan siyasar yankin ma albarka.

Ta gina fanfunan ruwa na sola kusan dukkan unguwannin Malam Madori ga kuma ɗinka kayan makaranta sama da dubu biyu ga makarantar da ta gama.

Ko a ‘yan kwanakin baya farfesa ta taɓa aiko da tirelar Shinkafa domin rabawa marasa ƙarfi. Ga kuma Makarantar koyon sana’a ga Mata da ta gina a garin na Malam madori.

Masu sharshi kan al’muran Siyasa na kallon wannan a matsayin wata dama ga Farfesa Hafsat Ganduje wajen dalewa ƙaragar Mulki a zaɓen 2023 mai zuwa.