Da alamu an kammala babban zaɓen 2023

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Biyo bayan gudanar da kammala zaɓen gwamna a jihar Adamawa, Kebbi da na ‘yan majalisa a wasu jihohin da a ka gudanar a makon jiya, alamu na nuna an kammala babban zaɓen 2023. In ban da kimanin jihohi 7 duk sauran jihohin na samun zaɓensu tare ne don ba a samu wani dalilin shari’a da ya sauya lokutan ba.

Kai tsaye hankali zai koma kan waɗanda za su shigar da qara kotu don ƙalubalantar sakamakon zaɓen. A ɓangaren zaven shugaban ƙasa dama tuni PDP da ɗan takarar ta Atiku Abubakar su ka shigar da ƙarar rashin amincewa da sakamakon. Ita ma jam’iyyar Leba da ɗan takarar ta Peter Obi sun shigar da ƙarar.

Aƙalla akwai wasu jam’iyyun da su ka haɗa da APM da ke cikin ƙarar don neman a soke sakamakon zaɓen. Kotun ɗaukaka ƙara kan zama nan ne a ke shigar da irin wannan ƙara ta zaɓen shugaban ƙasa inda bayan yanke hukunci duk wanda bai gamsu ba sai a nufi Kotun Ƙoli shikenan duk yadda ta kasance daga nan sai dai a jira wani zaɓen.

Zaɓen dai kamar yadda masu sharhi har ma da masu zaɓen kan su za su amince shi ne ya zama mafi samun ƙalubalen amfani da bambance-bambancen addini da kuma ƙabilanci a wani ɓangaren tun dawowa sabuwar dimokraɗiyya a 1999.

Hakan ya so kawo raba kan ‘yan ƙasa ainun a lokacin da a ke matuƙar buƙatar kawowa talakawa ɗauki. Yayin da talakawa ke cikin matuƙar ƙuncin rayuwa sai kuma a ka samu wannan illa da ‘yan siyasa su ka shigo da ita don dabarun lashe zaɓe.

Talakawa na fama da matsalar rayuwa amma a haka za su jure don biyan muradun su na wannan bambanci. Talakawa kan shata dagar shiga gasa don nasara kan juna kan addini, ƙabilanci da wani lokacin ɓangaranci. Babban ma shi ne addini don duk abun da ya shafi imani ya kan yi tsanani a zuciyar mutane kuma ba a iya shawo kan lamarin sai in jagororin addinin sun yi magana don fahintar da mabiya ga gaskiyar lamari ta hanyar gujewa tada fitina da ka iya kawo matsala ga musamman talakawa.

Idan talaka ba ya son kan sa ko ba ya son ɗan uwan sa talaka sai ka ga in bai hankali nesa ba sai ya zama zuga-zugin kunna wuta don kare muradun ‘yan jari hujja da ba abun da kan hada su da talaka sai lokacin zaɓe. Fakewa da abun da mutane ke ra’ayi wajen jan hankalin su a zabe alhali ba don taimkawa rayuwarsu ba ne na da matuƙar illa ko hakan kan zama babbar yaudara.

In an kuma duba da kyau za a ga a wani yanayin kowa na yaudarar kowa ne. In ma an ce ba haka ba to wasu talakawan sun zaɓi su yaudari kan su da kan su don cimma muradun abun da zuciyarsu ke so. Masu iya magana sun yi gaskiya da su ke cewa so hana ganin laifi.

Zuwa yanzu hankali ya ɗan fara kwantawa wajen tunanin ko akwai masu shirya maƙarƙashiyar ture dimokraɗiyya don kafa gwamnatin riƙon ƙwarya. In za a tuna hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS ta fitar da wannsn labari da gargaɗin masu ƙulla neman kafa gwamnatin da cewa su warware manufar.

Duk da ba a bayyana mutanen masu son hana rantsar da sabuwar gwamnati ba, an yi ta yaɗa irin waɗannan bayanai na yunƙurin. A nan ba za mu zurfafa ko amfani da bayanan bayan fage kan wannan zargin ba. Kasa dai a zahiri na zaune lafiya kuma a zaɓaɓɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin shan rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan gobe.

Aƙalla dai mutanen ɗan takarar jam’iyyar Leba na buƙatar kotu ta dakatar da rantsar da Tinubu har sai an yanke hukuncin ƙarar da su ka shigar. Kazalika ko kotun ta yanke hukunci kan zaɓen gabanin rantsarwar. Za a cigaba da zuba ido don ganin sakamakon da zai fito kan wannan ƙara da ta haɗa da fiye da ɗan takara ɗaya.

A kammala zaɓen da da a ka gudanar na jihohi biyu za a iya cewa an samu canjaras don APC ta lashe jihar Kebbi yayin da PDP ta samu nasarar tazarce a Adamawa. Haƙiƙa zaɓen na Adamawa ya fi ɗaukar hankali don yadda mace Hjaiya Aisha Dahiru Binani ta ƙalubalanci gwamna mai ci kuma ta taɓuka abun kirki wajen samun ƙuri’u masu yawa.

Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta ayyana gwamnan Adamawa Umar Fintiri na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe da samun tazarce a karo na biyu a mulkin jihar.

Babban jami’in kula da zaɓe na jihar Farfesa Mele ya bayyana sakamakon bayan kammala tattara sauran sakamakon zaɓen.

Farfesa Mele ya ce Fintiri ya samu auri’a 440, 861 da hakan ya ba shi nasara yayin da ita kuma Aisha Binani da ke bin sa a baya ta samu ƙuri’a 398, 788.

A murnar samun nasara Fintiri ya ce ba da Aisha Binani ya yi hamayya ba amma da wasu da ya ce manyan ‘yan siyasa a Abuja da ke son kawo sauyin mulki a jihar.

Haƙiƙa nasarar Fintiri ta kawo juyayin gaske musamman tsakanin masu marmarin samun lashe zaɓen mace ta farko ta zama gwamna.

INEC ta miqa bincike kan kwamishinan zaɓe na Adamawa ga babban Sufeton ’Yan Sanda:

Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta mika batun binciken kwamishinan ta na zaɓe a Adamawa Barista Ari Hudu ga babban sufeton ’yan sanda Baba Usman Alƙali don ɗaukar matakin da ya dace na doka.

Hukumar tun farko ta dakatar da kwamishinan don samun sa da laifin ayyana sakamakon zave ba tare da hurumin yin hakan ba.

INEC dai ta gana da dukkan masu ruwa da tsaki na lamarin zaɓen na Adamawa bayan hatsaniyar da ta auku; inda magoya bayan ’yar takarar APC Aisha Binani ke nuna gamsuwa ga ayyana su a matsayin waɗanda su ka lashe zaɓe yayin da ɓangaren gwamnan jihar Umar Fintiri na PDP ke cewa an yi mu su murɗiya.

Jami’a a sashen labarun hukumar Zainab Aminu ta ce hukumar na ɗaukar dukkan matakan da su ka dace bisa dokokin zaɓe don duba batun rawar da kwamishina Hudu ya aikata kuma an miƙa ragama ga babban sufeton na ‘yan sanda ya yi bincike don daukar matakin shari’a in har an samu Hudu da laifin da a ke tuhumar sa na riga Malam masallaci.

Duk da gamsuwa da dakatar da kwamishina Hudu Ari, wakilin gwamna Fintiri a ɗakin tattara sakamako Dr. Idi Hong na buƙatar ɗaukar matakan shari’a kan kwamishinan “ai kamata ya yi a ce tuni Hudu na gidan yari in ya so a ci gaba da gudanar da bincike, domin matsalar Nijeriya wasu kan yi laifi amma ba a hukunta su. In an bar irin wannan ya cigaba to wataran za a wayi gari ba a yi zaɓe ba ma sai a aiyana wanda za a ce ya lashe zaɓen.”

Magoya bayan Binani a Abuja na musanta zargin ba da toshiyar baki ga jami’an zaɓe bisa wani faifan bidiyon tuhuma da ke yawo a yanar gizo.

Bara’atu Garba Yusuf na kan gaba a masu nuna Aisha Binani ba ta yi wani abu na taka doka ba “abu kamar wasan kwakiwayo, sam Binani ba ta ba wa kowa komai ba wannan ma ai hankali ba zai dauka ba, ba abun da ya haɗa mu da wannan zargi.”

Masanin harkokin siyasa na jami’ar Abuja Dr. Farouk BB Farouk ya ce da alamun badaƙala na ƙara tagaiyara tsarin zave a Nijeriya ”da masu ba da toshiyar baki da waɗanda a ke ba wa duk na iya shiga ruɗani don yadda lamuran su ka rikice na zaɓe a Nijeriya. Lalle sai an ɗauki mataki na gaske kafin adalci ya riƙa samuwa a zaɓe.

Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta miƙa takardar shaidar lashe zaɓe ga gwamnan Adamawa Umar Fintiri.

INEC ta miƙa takardar a Abuja ne maimakon yadda ta saba yi daga jiha don dakatar da shugaban hukumar a jihar Barista Hudu Ari da ya dace ya miƙa shaidar.

“Ina mai ba da haƙuri ga cin zarafin da a ka yi wa ɗaya daga kwamishinonin zaɓe wato Farfesa A.A Zuru da a ka ɗauka ko shugaban hukumar ne Hudu,” inji Gwamna Fintiri bayan karɓar takardar shaidar.

Umar Fintiri ya nuna takaicin abun da ya zayyana da wasu ‘yan siyasar Abuja da ya zarga da hargitsa zaven jihar fiye ma da batun fafatawarsa da Aisha Binani ta APC.

Game da bin kaɗun Farfesa Zuru da a ka kwaɓe ma sa kaya, gwamna Fintiri ya aza alhakin ga waɗanda ya zayyana da zauna gari banza inda ya yi tayin tallafa wa Farfesan a madadin diyya.

Yanzu za a jira a ga mataki na gaba na ɓangaren ‘yar takarar APC Aisha Binani ko za ta rungumi ƙaddara ko kuma za ta garzaya kotu.

Kammalawa;

Shawara ɗaya ga talakawa da ke matuƙar marawa jam’iyyu baya, to gaskiya ita ce kar su bari hamayyar siyasa ta raba su da juna ko ta zama sanadiyyar ƙiyayya da rashin ganin mutuncin juna. Da za a raba siyasa da hulɗa ta yau da kullum musamman a tsakanin magoya baya ko talakawa da hakan ya fi zama zaɓi nagari.