Zan ci gaba da biyan korarrun ‘yan sandan da ke rakiyata albashi – Rarara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shahararren mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin ‘yan sandan nan guda uku da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kora bisa laifin harba bindiga ba bisa ƙa’ida ba da kuma rashin sanin makamar aiki.

Manahaja ta ruwaito cewa ‘yan sandan da ke tsaron Rarara sun shiga cikin matsala bayan wani faifan bidiyo da ya nuna yadda suke harba bindiga a sama, a wani mataki na nuna ƙarfin tuwo ga abokan hamayyar mawaƙin.

Rundunar ta ce bayan bincike, ta samu Insifekta Dahiru Shuaibu, Sajan Abdullahi Badamasi da Sajam Isah Danladi da laifi kuma daga baya aka kore su.

Da ya ke magantuwa a kan korar da aka yi musu, mawaƙin ya sha alwashin ci gaba da sauke nauyin da ke kansu da suka haɗa da biyansu albashinsu na wata-wata.

Sai dai ya ce ya na roƙo ga rundunar da ta yi musu sassauci.

“Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kori jami’an tsaro na. Bayan sun sanar da ni sai na tambaye su ko nawa ne albashin su a ’yan sandan Nijeriya, sai suka gaya mini.

“Kuma na yi masu alƙawari cewa, daga yanzu, zan ci gaba da biyansu albashin da rundunar ‘yan sanda ke biyansu.

“Sun ɗaukaka ƙara kan korar da aka yi musu, kuma idan sun yi nasara, za a iya mayar da su bakin aiki, idan kuma a ƙarshe hakan bai faru ba, zan ci gaba da biyansu.

“Na tuntuɓi mutane daban-daban domin su shiga maganar, tun kafin a kore su, amma duk da shiga tsakani da roƙon da na yi wa ‘yan sanda, amma rundunar ta dage kan korarsu,” inji Rarara.