Da Dumi-Dumi: Matatar Dangote ta sake rage farashin fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake cigaba da gasar farashi tsakanin kasuwannin man fetur na cikin gida, Matatar Dangote ta sake rage nata daga N835 zuwa N820 ga kowace lita.

A watan da ya gabata ne matatar, wadda ke da sararin fitar da ganga 650,000 a kullum, ta rage zuwa N835 daga N865.

Ragin na yanzu na nufin kara wa kwastomominta daraja da kuma karfafa matsayinta a kasuwa.

By Babaji