ASUU ta zabi Farfesa Piwuna a matsayin sabon shugabanta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya (ASUU), ta zabi Farfesa Chris Piwuna a matsayin sabon shugabanta.

Piwuna babban likita ne a bangaren kula da mahaukata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, wanda ya karbi ragamar jagorancin kungiyar daga hannun Farfesa Victor Osodeke na bangaren Ilimin ƙasa (soil science) daga Jami’ar Harkokin Noma na Michael Okpara dake Umudike a Jihar Abia.

Farfesa Piwuna shi ne shugaban bangaren kula da lamuran dalibai na Jami’ar Jos.

An zabe shi ne a lokacin da aka gudanar da babban taron kungiyar karo na 23 a Benin babban birnin jihar Edo, ranar Lahadi.

Haka kuma an fafata ne a zaben tsakanin sa da Farfesa Adamu Babayo na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Jihar Bauchi.

Hakan na zuwa ne kwanakin kadan ana yada jita-jitar shirin shiga yajin aiki da kungiyar ke yi bisa rashin biyan mambobinta kudaden alawus.

By Babaji