
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya halarci taron jagororin Jam’iyyar PDP da ya gudana a Abuja.
An gudanar da taron ne a masaukin baki na Gwamnan Jihar Bauchi dake unguwar Asokoro a birnin, ranar Lahadi.
Zaman shi ne na farko tun bayan da Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya fice daga jam’iyyar zuwa APC.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da: Ademola Adeleke (Osun); Caleb Mutfwang (Filato); Bala Mohammed (Bauchi); Seyi Makinde (Oyo); Ahmadu Fintiri (Adamawa); Peter Mbah (Enugu); Dauda Lawal (Zamfara), da kuma Kefas Agbu (Taraba).
Haka kuma tsofaffin gwamnonin da suka halarta sun hada da: Ahmed Makarfi; Seriake Dickson; Olagunsoye Oyinlola; Achike Udenwa; Liyel Imoke; Ifeanyi Ugwanyi (Enugu); Okezie Ikpeazu (Abia); Samuel Ortom (Benue); Idris Wada (Kogi) Babangida Aliyu (Neja); Adamu Muazu (Bauchi); Udom Emmanuel (Akwa Ibom); Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato); Gabriel Suswan (Benue); Abubakar Bukola Saraki (Kwara); Sule Lamido (Jigawa), da kuma Ibrahim Dankwambo (Gombe).
Mambobinta na Kwamitin Ayyuka na ƙasa (NWC) sun haďa da Shugaban rikon kwarya, Amb. Umar Damagum; Sakataren shirye-shirye, Umar Bature; da kuma Mashawarci kan harkar Shari’a, Kamardeen Ajibade.
Saidai, tsohon mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar bai samu halarta ba.
Ana ganin zaman ba ya rasa nasaba da kokarin samar da hanyoyin warware matsalolin rarrabuwar kai a tsakanin ƴaƴan jam’iyyar musamman duba da yadda ake shirin tunkarar babban zaben 2027.
