EFCC za ta cakfe Tompolo bisa bidiyon wulaƙanta Naira

Spread the love

Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana shirin kama tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan fashin teku na Neja-Delta, Chief Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, bisa zargin wulaƙanta naira a wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta. A bidiyon, an ga wani mutum na yayyafa masa kuɗi na N1,000 yayin bikin cikar sa shekara 54 da haihuwa.

Bidiyon da wani mai amfani da sunan #harreceipts ya wallafa a dandalin X.com ya janyo cece-kuce daga ‘yan Najeriya da suka zargi EFCC da son kai wajen aiwatar da doka. Wasu sun bayyana cewa hukumar ba za ta iya kama Tompolo ba saboda matsayin sa a cikin al’umma, kamar yadda aka saba gani a wasu lokuta da shahararrun mutane ke wulaƙanta naira ba tare da hukunci ba.

Sai dai EFCC ta mayar da martani inda ta wallafa hoto daga bidiyon tare da rubutu mai cewa, “Babu wanda ya ƙarfin doka. Tompolo zai amsa tambayoyi.” Wannan na zuwa ne bayan kama Bobrisky da E-Money kan irin wannan laifi. Jama’a na ci gaba da sa ido kan matakin da hukumar za ta dauka domin tabbatar da adalci da daidaito.

By ukarofi