Da hannun masu POS wajen tura wa masu garkuwa kuɗin fansa – Gwamnatin Nijeriya

Spread the love


Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja


Cibiyar yaƙi da ta’addanci (NCTC) a ƙarƙashin ofishin mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro (ONSA) ya ce, masu hada-hadar kuɗi da injin POS suna taimakawa wajen biyan kuɗin fansa da ake bai wa ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
Babban ko’odinetan cibiyar Adamu Laka, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin taron manema labarai na ƙarshen shekara a Abuja.
Laka, wanda manjo-janar ne a rundunar sojin Nijeriya, ya bayyana hakan ne a yayin da ake sake fuskantar barazana ta tsaro. Manyan ƙungiyoyin ta’addanci sun zafafa hare-hare da garkuwa da mutane a Arewacin Nijeriya musamman yara ‘yan makaranta da masu ibada.
A watan Nuwamba, an yi garkuwa da ɗaliban makarantar Kebbi da Neja. Sai dai daga baya waɗannan ɗalibai sun shaƙi iskar ‘yanci.
Duk da cewa gwamnatin Nijeriya ta nuna ƙyamarta game da biyan kuɗin fansa ga ‘yan bindiga, sai dai ‘yan uwan waɗanda ake sacewa kan biya kuɗin fansar domin a sakar musu ‘yan uwa. Sannan akwai zargin cewa gwamnati na biyan masu garkuwa da mutane domin su saki waɗanda suka kama, sai dai gwamnati ta musanta wannan zargin.
Laka ya ce bincike kan garkuwa da ayyuka da suka shafi ta’addanci sun nuna yadda ake biyan kuɗin fansa ke da alaƙa da masu POS, wanda ke bai wa masu irin wannan munanan ayyuka damar cirar kuɗi da kaucewa bindiddigi.
“A wasu lokutan ana tura kuɗin fansar ne kai tsaye ta POS kuma masu garkuwa da mutanen ne ke ba da lambar asusun,” ya faɗa. “Daga nan sai su cire kuɗin.”
Laka ya ce, ana ƙoƙarin ganin an magance wannan matsala.
Manhaja ta gano yadda sana’ar POS ta ƙara yawa a ‘yan shekarun baya-bayan nan sakamakon rashin bankuna a yankunan karkara da tsare-tsare na rashin ba su dama daga CBN.
Dubbun nan masu amfani da POS ne ke cira da turawa da biyan buƙatu na kuɗi a madadin bankuna da suke gudanar da ayyukansu ba tare da wani tsari a hukumance ba.
Duk da cewa mutane da dama sun samu damar gudanar da hada-hadar kuɗi cikin sauƙi, amma ya haifar da barazana kamar irin wadda mista Laka ya ambata.
CBN ya ba da umarni daban-daban domin tafi da harkokin masu POS da sauran ejan-ejan da suka haɗa da “Ka san kwastamanka” (Know Your Customer, KYC) wanda ya buƙaci bankuna da su kula da hada-hadar kuɗinsu da gaggauta sanar da hukumar tattara bayanan sirri (NFIU) idan suka lura da wani abu da ba su gamsu da shi ba.
A ƙarƙashin dokokin, ejan na POS ana son gudanar da ayyukansu bisa ƙa’idar da aka ɗibar musu da tantance waɗanda suka bai wa POS da kuma ajiye bayanan hada-hadar kuɗi na kwastamominsu. Sannan an buƙaci bankuna da su rufe asusun da suke da alaƙa da wasu masu aikata ta’addanci.
Kira ga manema labarai:
NCTC ta buƙaci kamfanonin yaɗa labarai da su yi takatsantsan wajen sanar da bayanan da suke da alaƙa da tsaro suna gargaɗin cewa irin gaggawar sakin labarai zai iya kawo tarnaƙi ga ayyukan jami’an tsaro da jefa rayuka cikin haɗari.
A yayin da yake yaba wa manema labarai kan nuna ƙwarewa, Mista Laka ya ce, fitar da sahihin rahoto abu ne ya taimaka wajen yaƙi da ta’addanci da ƙarfafa guiwar al’umma da kuma jan hankalin gwamnati wajen magance ta’addanci da sauran barazana ta rashin kwanciyar hankali a Nijeriya.
Sai dai ya ce, lokacin tura labarai nan take da son zarce kowa a dandalin sada zumunta ya ce saboda tasirin da labarai ke da shi da sha’anin tsaro.
Ya ce, cibiyar ba tana kira da a tsuke baki ba ne, sai dai akwai buƙatar kula da abin da za a wallafa nan take da da kuma abin da ya kamata a yi takatsantsan a kai saboda kare al’amuran tsaro na ƙasa.
Mista Laka ya yi gargaɗin cewa wallafa wani labari da gaggawa na iya zama sanarwa ga masu aikata munanan laifuka da ake zargi da zama cikas ga binciken da ake yi, da lalata shirin kakkaɓe ‘yan ta’adda.
Mista Laka ya ce ‘yan ta’adda da sauran ƙungiyoyi makamantansu suna sake ɓullo da dabaru wanda ke buƙatar a samar da tsari mai ƙarfi na tattara bayanan sirri da sadarwa da kuma haɗin kan al’umma.
A yayin da yake ba da amsa game da batun kutse ta iyakokin Nijeriya, ya ce, cibiyar na haɗa kai da sauran jami’an tsaro domin magance barazanar da ke ratsawa ta yankin Sahel.
A cewarsa, ƙungiyoyi kamar Lakurawa Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) sun kutsa wasu sassa na Arewa masi yamma da Arewa ta tsakiya, wanda ya ta’azzara matsalar tsaro a iyakokin garuruwa da suke.
Laka ya nuna damuwa game da amfani da dandalin sada zumunta da ‘yan ta’adda ke yi wajen yaɗa farfaganda, yana mai cewa akwai shafuka da yawa da suke da alaƙa da ‘yan ta’adda.
“Mun gano akwai shafuka da dama da suke TikTok, Instagram, Snapchat, Facebook da ɗ da suke da alaƙa da ‘yan ta’adda” ya bayyana.
“Suna son kasuwancinsu ne ya bunƙasa, amma za mu tunkare su saboda irin illar da abubuwan da suke wallafawa da tabbatar da an cire su,” ya faɗa.
A jawabinsa na rufewa, ya bayyana kafafen yaɗa labarai da zama za zama muhimmiyar hanya ta yaƙi da ta’addanci, yana mai buƙatar ‘yan jarida da su hana ‘yan ta’adda samun gurbi yaɗa manufofinsu da bai wa al’umma tabbacin irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen kare su.

By ukarofi