Da kyakkyawar manufa muka horar da sojoji mata – Rundunar Sojin Saudiyya

Rundunar sojoji ta Ƙasar Saudiyya ta ce, da kyakkyawar manufa ta bai wa sojoji mata horo don ci gaba da yi ƙasar hidima yadda ya kamata.

Babban jami’i na rundunar, Maj. Gen. Adel Al-Balawi, shi ne ya bayyana haka a wajen bikin yaye sojoji mata karon farko a Saudiyya a Larabar da ta gabata.

Al-Balawi ya ce cibiyar bai wa mata horon an tsara ta daidai da na ƙasa-ƙasa wadda ake sa ran za ta taimaka wa rundunar sojojin ƙasa cimma buƙatunta a gaba.

Wannan shi ne karo na faro da Ƙasar Saudiyya ta bai wa mata damar shiga aikin soja a ƙasar inda kuma ta yaye rukunin farko bayn shafe makwanni 14 suna karɓar horo na musamman.

Daga bisani, sojojin sun sha rantsuwar kama aiki, tare da yi wa wasu daga cikin su kyauta ta musamman saboda bajintar da suka nuna yayin karɓar horo.