Dakarun tsaro sun tarfa Bello Turji a wata musayar wuta

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an tsaro da mafarauta sun yi arangama da jagoran ƴan bindiga, Bello Turji a garin Gatawa dake ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato yayin da suka tarfa shi a bayan waɗansu duwatsu.

A safiyar ranar Talata da misalin ƙarfe 6 na safe ne aka samu rahotonni da dama daga garin waɗanda suka ce an samu musayar wuta a tsakanin dakarun da ƴan bindiga.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, ƴan bindigar sun yi yunƙurin shiga garin ne inda sojoji da mafarauta suka dakatar da su.

Ya ce, babu cikakken bayani game da sakamakon artabun, amma su na fatan jami’an tsaron za su yi galaba akan ƴan ta’addar.

Haka ma wani da bai amince a wallafa sunansa ba, ya ce ba su taɓa ganin irin fafatawar ba a baya a garin, ya na mai cewa su na fatan wannan ya yi sanadiyyar mutuwar Bello Turji.

Duk da cewa ana zargin Bello Turji da zama a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, amma ayyukansa sun bazu zuwa ƙananan hukumomin Sabon Birni, Isa da Goronyo a Sakkwato.