Dalilai bakwai da suka sa ‘yan Kwankwasiyya suke da wahalar sha’ani

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN

1: Duk kyan abu da tsarinsa, in har ba ‘Yan Kwankwasiyya ne suka kawo shi ba, to a wajen galibin ‘yan kwankwasiyya wannan abun mammuna ne, abin ƙyama ne, sannan abun a yi watsi da shi, ko rushe shi ne. Sannan duk wani abu duk muninsa, in har Kwankwasiyya ce ta kawo shi, to a wajensu wannan abu ne mai kyau, abu ne da zai kawo ci gaba ko da kuwa cikin ƙoƙon zuciyarsu sun san ba haka ba ne.

2: A tunanin galibin ‘yan Kwankwasiyya shi ne, duk mai adawar siyasa da su, to maƙiyi ne, mahassadi ne, kuma bagidajen da ba ya son ci gaba, sannan su a nasu ɓangaren adawar su ga kowani abokin adawar siyasar a wata gwagwarmayar qwato ‘yancin al’umma ne, kuma abin da ya fi dacewa!

3: In ka bayyana ra’ayinka in har bai yi dai-dai da tsarin Kwankwasiyya ba, to galibin ‘yan Kwankwasiyya kallonka suke a ɗan Gandujiya, kuma a wajensu yin adawa da Kwankwasiyya kamar dai goyon bayan Gandujiyya ne da tavargazar Gwamnatinsa. Ko da kuwa ba ka da alaqa da Gandujiyya da aika-aikar Gwamnatinsa.

4: Galibin ‘yan Kwankwasiyya tunaninsu shi ne son Kwankwasiyya shi ne kishin Kano, adawa da Kwankwasiyya qin jahar Kano ne. Su a ganinsu yau in mutum ba ɗan Kwankwasiyya ba ne, to maliyin Kano ne, ko kuma kawai ma ba ɗan Kano ba ne, ko da kuwa jikan Kano Maƙeri ne!

5: A tunanin galibin ‘yan Kwankwasiyya, wannan Gwamnatin tasu ce su, su kaɗai, sauran ‘yan Kano ba su da hakki a kan Gwamnatin nan, don haka, duk aika-aikan da Gwamnatinsu ta yi dai-dai ne, ko da hakan zai cutar da sauran mutanen Kano.

6: Makauniyar soyayya, misalin dai yadda aka yi wa Buhari makauniyar soyayyya a shekarun baya musamman farkon hawan mulkinsa, da zarar ka ga aibu ka yi magana, sai a dirar ma du sunaye kala-kala da baƙaƙen maganganu, yanzu ma a kan haka ake, duk wata maganar gyara ko hannunka mai sanda da za ka yi wannan Gwamnatin to galibin ‘yan Kwankwasiyya a shirye suke su faɗa maka baƙaƙen maganganu.

7: Gaskiyarsu ita ce gaskiya, fahimtarsu ita ce m afi dacewar fahimta, gaskiyar waninsu shirme ce, abar jefarwa. Sannan babu fahimta sahihiya mai kyau, sai tasu.

Wannan dalili guda bakwai su ne, abubawan da ya sanya galibin ‘yan kwankwasiyya ke da wuyar sha’ani.

*Adalci, ba duka ‘yan kwankwasiyya ba ne ke da wannan halayyar, akwai masu tsage gaskiya, sai dai ba su da yawa!

Nan gaba Insh’ Allahu zan yi rubutu a kan “Illar Uban Gida a Siyasar Jahar Kano”

Mukhtar Mudi Sipikin, marubuci/manazarci ne. Ya rubuto daga jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *