Daga USMAN KAROFI
Fitaccen lauya kuma babban lauyan Nijeriya (SAN), Wahab Shittu, ya bayyana cewa tsauraran dokokin da ake bi wajen fitar da wanda ake zargi daga wata ƙasa zuwa wata su ne suka hana gwamnatin Najeriya shari’ar tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke, tsawon sama da shekaru takwas.
Alison-Madueke, wadda ake zargi da wawure miliyoyin daloli na dukiyar ƙasa yayin da take rike da muƙamin minista a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, ta bar Nijeriya zuwa Birtaniya tun bayan ƙarshen wa’adin gwamnatin Jonathan. Duk da shigar da ƙara a kotunan Najeriya, an kasa samun damar gabatar da ita don amsa tuhumar.
Da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin Channels a ranar Juma’a, Shittu ya ce tsauraran matakan shari’a da na ƙasa da ƙasa da ake buƙata wajen dawo da wanda ya tsere daga wata ƙasa zuwa wata ne suka hana shari’ar. A cewarsa, “Akwai matakan shari’a da dole ne a bi, tare da wasu ƙa’idojin gudanarwa na ƙasa da ƙasa da ake buƙatar cika kafin a dawo da mutum daga wata ƙasa zuwa Najeriya.” Wannan, a cewar sa, shine babban ƙalubalen da gwamnatin Nijeriya ke fuskanta a wannan batu.