Dalilan da suka sa na bugawa marubutan online littafi – Jibrin A. Rano

“Daga manazarci ake zama marubuci “

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kawo yanzu kusan duk wani marubucin yanar gizo ko na online yana da labarin vullar wani mataimaki mai kishin cigaban adabi da rayuwar marubuta, wanda ya fito da wani tsari na tallafa wa marubutan online, ta hanyar buga musu littafin su na farko, don su ma su shiga sahun marubuta masu buga littafi. A cewarsa, burin kowanne mai rubutu ne a kira shi da marubuci, don haka bai dace a riƙa kallon waɗanda ke rubutu ta yanar gizo a matsayin ba cikakkun marubuta ba. A saboda haka ne ya ke ganin idan su ma aka fara ganin littafinsu a kasuwa, za a rage wariyar da ya ce ana nuna musu. Wakilin Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya zanta da wannan jajirtaccen marubuci mai kishin zama lauya, da ake kira da Barista Jibrin Adamu Rano, daga Jihar Kano. A sha karatu lafiya!

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanka.

JIBRIN RANO: Sunana Jibrin Adamu Jibrin Rano, wanda ake yi wa laƙabi da Barista.

Mai ya sa ake kiran ka da Barista, kai lauya ne?

Ni ba lauya ba ne, amma ɗalibin ilimin shari’a ne. Na daɗe Ina da muradin na gaji mahaifina na zama lauya tun Ina ƙarami. Shi ya sa abokaina suke kirana da Barista.

Ko za ka ba mu tarihin rayuwarka a taƙaice?

Mai zai hana? An haife ni ne a garin Jos, a wata Unguwa da ake kira Nasarawa, yankin Ýan Shanu, a shekarar 1990. Na fara karatun firamare da na allo a garin Jos, kafin daga bisani da muka koma Kano a ƙaramar Hukumar Rano, inda nan ne asalin tushen iyayena, a can na qarasa karatuna na firamare da sakandire. Daga nan kuma na cigaba da karatun Diploma aɓangaren nazarin ilimin Shari’a, na gama a shekarar 2014, sai dai Allah bai nufa na ci gaba da karatun ba.

Menene tarihinka a harkar rubutun adabi?


Yawanci daga manazarci ake zama marubuci, ni ma ɗin haka ne. Na fara karatun labarai na Hausa tun ina aji huɗu na firamare, bayan na ƙara wayo sai na ji nima Ina sha’awar na rubuta nawa. Na fara rubutawa Ina karanta wa abokaina na aji, tun Ina aji uku na sakandire, tsakanin shekarar 2006 zuwa 2007 kenan. Sai dai a lokacin da karatun da rubutun duk na yaqi nake yi, na fara rubuta wanda ba na yaqi ba a kan wani labarina ‘Mafiya’ a shekarar 2011, wanda labari ne da ya shafi harkokin shari’a.

Ka taɓa rubuta littafi ne? Ba mu labarin wasu daga cikin su?

Na tava rubuta labarai ba guda ɗaya ba. Daga cikin labaran da na rubuta akwai labarin ‘Da Ma Sun Faxa Min’. Labarin da ya yi na ɗaya a gasar marubuta ta ƙasa da Gusau Institute suke sakawa duk shekara, labarin ne ya ciri tuta a shekarar 2020, inda ya ciyo kuɗi Naira 250,000. Na sake shiga gasar Abubakar Imam Hausa Fiction Competition a Kano a shekarar 2021 da labarin, ya kuma sake yin nasara ya ciyo Naira 200,000. Ina da wasu labaran da na ci wasu gasar da su. A taƙaice dai Ina da dogayen labarai guda 14 a yanzu, da kuma gajeru da ɗan dama.

Wacce gudunmawa ka ke bayarwa a harkar cigaban adabin Hausa?

Zan faɗa ba don fariya ba, duk wani marubuci mai tasowa da na gani yana buƙatar wata shawara, ko dabara, ko zaburarwa to, Ina ƙoƙarin yi masa a matsayin gudunmawar da za mu taru mu cicciva Adabin Hausa tare. Har maƙalu da dabarun rubutu nake yi, wanda in dai har ka yi bincike ƙarƙashin taken Dabarun Rubutu manhajar Google da ake yi wa laƙabi da matambayi ba ya ɓata, zai yi wuya idan ba su nuna maka nawa ba. Baya ga haka akwai aji na musamman a whatsapp da muke nazari da ire-irena don koyawa matasan marubuta dabarun rubuta labari.

Kwanaki ka yi wani rubutu a shafinka na Facebook, inda ka yi alƙawarin ɗaukar nauyin buga littafi ga marubutan da ba su tava buga littafi a rayuwarsu ba, ƙarƙashin wasu sharuɗɗa, menene ya ba ka ƙwarin gwiwar yanke wannan shawara?

Dalilan guda biyu ne. Na farko na san cewa, rubutu wata baiwa ce da duk mai ita yake yin alfahari da ita, duk mai ita yana so ya ji cewa an kira shi da suna marubuci. Sai dai da yawan marubuta sun rasa wannan damar da za a kira su da marubuta, ba don komai ba sai don kasancewar nasu rubutun a iya yanar gizo ko kuma kamar yadda ake cewa online suke yin sa, ba su taɓa buga littafi ba. Irin wannan wariyar da marubutan ɗab’i suke yi ne ya tunzira ni na ji cewa duk wani wanda na gani yana da baiwar abin, zan saka masa wasu sharuɗɗa waɗanda in dai har ya kiyaye su zan buga masa labarinsa, don shi ma ya dinga amsa sunan marubuci irin yadda duk wani mai taqama da sunan zai yi.

Dalilina na biyu kuma shi ne; ni ma labarina na farko da aka fara bugawa a duniya, ba ni ne na buga shi da kuɗina ba, wani ne ya buga min. Don haka irin daɗin da na ji lokacin da aka buga min nake so na jiyar da tarin marubuta masu tasowa in sha Allah. Sannan Ina fata yadda su ma suka ji daɗi wata rana su jiyar da waɗanda ba su ji ba.

Kawo yanzu marubuta nawa ne suka samu shiga wannan tallafi?

Marubutan ba su da yawa, mutum takwas ne kacal, sai kuma mutum uku da nake fatan nan ba da daɗewa ba su ma a yi nasu aikin in sha Allah.

Menene burinka na ayyana ɗaukar wannan nauyi, da ba kowa ne zai iya ba?


Burika uku gare ni. Na farko, na zama wani tsani da zai dinga kai marubuta ga cikar burinsu na zama cikakkun marubuta a wurin masu nuna musu wariya. Na biyu, Ina fata na zama tamkar tsintsiyar da za ta share wa marubuta hanyar da za ta sada su da masu bugun littafi ‘yan gaske da ba za su yi musu kan-ta-waye ba. Na uku, kan-ta-waye da ake yi wa marubuta yana sare musu gwiwa da hana su buga littafansu. Ina fatan idan na share musu hanya harkar ɗab’i ta ɗan farfaɗo ko ba duka ba.

Akwai wani tallafi da kai ma ka samu ne ka ke so ka yi wannan aiki, ko wata ƙungiya ce take amfani da kai wajen taimaka wa marubuta?

Babu wani tallafi da wani, ko wata ƙungiya suka ba ni wajen yin wannan aikin. Da kuɗin aljihuna nake yi. Shi ya sa ba na gaggawa wajen yi, Ina yi ne duk lokacin da na samu yanayin yin hakan.

Faɗa mana sharuɗɗan da ka sa don marubuta masu sha’awar cin moriyar wannan tallafi naka?

Sharuɗɗan ba masu wuya ba ne. Muna son nagartaccen labari a kan kowanne jigo. Kawai dai labarin kada ya haura kalmomi dubu arba’in da biyar.

Shin kana ganin wannan tsarin naka zai taimaka wajen farfaɗo da harkar ɗab’in buga littattafai?

Ina fatan haka, in sha Allah. Don wasu cikin waɗanda muka fara aikin da su tuni sun zama ‘yan gari wajen buga labaransu da kansu.

Yaya ka ke ganin bugawa marubuta littafinsu na farko, zai taimaka wajen ƙarfafa musu gwiwa?

Na faɗa maka cewa ni ma buga min littafina na farko da aka yi ne ya fara ƙara min qwarin gwiwa, da busa min numfashin yin abin da aka yi min. Don haka ina fata su ma waɗanda aka yi wa ya zame musu tamkar ingarman dokin da za su hau su yi ta sukuwa a filin Adabi.

Wasu litattafan da Jibrin ya wallafa

Wanne saƙo ka ke da shi ga sauran manyan marubuta da masu hannu da shuni wajen samar da irin wannan tallafi ko gidauniya, don ceto harkar rubutun Adabi?

Masu hikima na cewa; “Ƙololuwar nasara ba ita ce kai kaɗai ka yi nasara ba, ƙololuwar nasara ita ce yawan mutanen da ka cicciɓa ku ka yi nasara tare”. Ashe kenan yana da kyau manyanmu su dinga ɗora mu a gwadaben da wata rana za mu yi alfahari da su, idan muka ga nasarar da muka samu a dalilin su.

Wanne buri ka ke so ka cimma nan gaba a wannan vangaren na raya harkokin adabi?

Alƙalami ya fi takobi kaifi, wannan wani azanci ne na Bahaushe. To, amma mai yake nufi? Yana nufin a maimakon jama’a su ɗauki makamai su yi ta yaƙar junansu, gara su ɗauki alƙaluma su yi rubutu na wayar da kan junansu. Burina kenan da rubutu, ina fata na zamo cikin jerin marubuta masu wayar da kan da idan suka nuna matsala da bakin alƙalaminsu a ce ƙurunƙus!

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?

A rayuwata ta rubutu aƙidata ita ce nagartar marubuci ba a yawan labarai ba ne, yana a yawan ma’anar rubutunsa. A rayuwa ta zahiri kuma; ina ji a raina in dai har abu rabona ne to, tabbas zai zo ya same ni a duk inda nake. Don kuwa rabon kwaɗo ba ya hawa sama, idan ya hau ma sai ya faɗo.

Mun gode da lokacinka.

Ni ma Ina godiya ƙwarai da gaske.