Daga UMAR GARBA a Katsina
Tun bayan rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa marigayi mallam Umaru Musa Yar’adua, jama’a da dama musamman a shafukan sada zumunta ke ta cece kuce game da rashin halartar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa, Hajiya Dada mai shekara kimanin 102 a duniya ta rasu a ranar Litinin da ta gabata a birnin Katsina.
Tun bayan samun labarin, tsofaffin shugabannin ƙasar nan irinsu Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo da mataimaka irin su Kashim Shettima, Atiku Abubakar, Namadi Sambo Yemi Osinbajo da kuma gwamnoni, ‘yan majalisa, ministoci da ma sarakunan gargajiya ke ta tururuwa zuwa gidan marigayiyar don yin ta’aziyya.
Hakan ne ya sa jama’a ke tambayar me ya hana tsohon shugaba Muhammadu Buhari halarta sallar jana’iza ko kuma zuwa yin ta’aziyya ga iyalan marigayiyar, duba da cewa ɗaya daga cikin ‘ya ‘yan marigayiyar wato Janaral Shehu Musa ‘Yar’adua aminin tsohon shugaban ne kuma abokinsa.
Sai dai mai taimaka wa Buhari kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Bashir Ahmad ya fito inda ya kare mai gidan na sa.
A cewar Bashir, Buhari bai samu damar halartar jana’izar ba saboda baya ƙasar nan a lokacin da aka yi rasuwar.
Tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasar, ya kuma musanta labaran da ke cewa da gangan Buhari ya ƙi halartar jana’izar ko zuwa ta’aziyya ga iyalan marigayiyar.
A cewar shi Hajiya Dada uwa ce ga Buhari duba da cewa mahaifiyar amininsa ce kuma abokin karatunsa, ya cigaba da cewa duk da tsohon shugaban bai samu damar zuwa gidan ba, amma ya aika da saƙon ta’aziyyarsa.
“Na ga rubuce rubuce dake yawo a shafukan sada zumunta da ke nuni da cewa Buhari yana Daura amma ya ƙi halartar jana’izar Hajiya Dada, mahaifiyar amininsa kuma abokin karatunsa, Janaral Shehu Musa ‘Yar’adua.
“Tsohon shugaban ƙasa (Buhari) a halin yanzu baya cikin ƙasar nan wanda wannan ne dalilinsa na gaza halartar jana’izar sai dai ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar” Inji Bashir Ahmad.
