Da ƊUMI-ƊUMI: Shettima ya gayyaci Ribaɗu da jagororin NNPCL kan tsadar man fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya gayyaci ƙaramin ministan Ma’aikatar Albarkatun Man fetur, Heineken Lokpobiri da shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa, (NNPCL) Mele Kyari.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA) Nuhu Ribaɗu na cikin waɗanda aka gayyata zuwa Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja kan tsadar man fetur.

Shettima na ganawa da manyan jami’an ne a ofishinsa da ke Fadar sakamakon ƙarin farashin man a ranar Talata daga N568 zuwa N855 da N897 la’akari da yankin da ake sayarwa.

Tuni dai ƴan kasuwa ke sayar da lita a sama da yadda NNPCL ke yi inda wasu ke sayarwa akan N1,200.

Hakan na zuwa ne bayan da NNPCL ya bayyana cewa ya na fuskantar matsalolin raba man fetur sakamakon ƙalubale na kuɗi da ya ke fuskanta.

By Babaji