Daga USMAN KAROFI a Abuja
Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin a ranar Alhamis ya bayyana goyon bayansa ga Kamala Harris a zaɓen shugaban ƙasar Amurka da za a gudanar a watan Nuwamba.
Putin ya bayyana hakan ne kwana guda bayan da ma’aikatar shari’a ta Amurka ta tuhumi wasu manyan ƴan jaridun Rasha biyu kan wani shiri da su ke na yin tasiri a zaɓen na Nuwamba da farfagandar goyon bayan Rasha.
Putin ya ce a farkon wannan shekarar, kafin Shugaba Joe Biden ya janye daga takarar shi wanda ba abun mamaki bane, ya fi son shi a kan Trump saboda Biden shugaba ne da ake saurin fuskantar ina ya dosa.
Shugaban Kremlin ya ce Biden ya ba da shawarar magoya bayansa da su goyi bayan Harris, “za mu yi haka, kuma za mu mara mata baya”.
Putin ya ce, Trump a matsayinsa na shugaban ƙasa, ya gabatar da ƙarin takunkumai kan Rasha fiye da kowa a fadar White House.
