Dalilin da ya sa muka ba wa kamfanin Hitech kwangilar titin Legas-Kalaba

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin da ya sa ta bai wa kamfanin Hitech Construction Company Ltd aikin gina titin Legas-Kalaba. Ministan ayyuka, Sanata Dave Umahi, ya bayyana hakan yayin ziyarar duba aikin a Legas a ranar Asabar.

Tun da farko tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya soki aikin da kuɗinsa ya kai naira tiriliyan 15.6, yana mai cewa aikin ya kasance almubazzaranci da cin hanci.

Minista Umahi ya bayyana cewa, akwai jita-jita da ke cewa ba a yi gasa wajen ba da aikin ba, amma ya ce dokokin Ƙasa sun amince da nau’ikan hanyoyi uku na sayen kaya ko ayyuka. Ya ce, lokacin da aka fara aikin, an nemi kamfanonin da ke da za su iya aikin guda biyar ko fiye, saboda kamfanoni masu irin wannan kayan aiki da za ai titin ba su da yawa a Najeriya.

Ya ce, an gano cewa kamfanin Hitech ya gudanar da irin wannan aiki a kan titin Oworonshoki zuwa Apapa, wanda suka yi nasarar kammala shi cikin inganci. Saboda haka ne aka tuntuɓi kamfanin domin gudanar da aikin sashi na farko.

Daga baya kuma, bayan wasu kamfanoni sun fara shigo da kayan aikin siminti, an bude sashi na biyu ta hanyar zaɓe na musamman, inda aka gayyaci wasu kamfanoni suka shiga cikin jerin masu neman kwangilar, kuma Hitech ya sake samun nasara.

Ministan ya jaddada cewa ba a karya doka ba wajen ba da aikin, kuma babu wani cin hanci ko son kai a cikin lamarin. Ya kuma yi bayanin cewa Shugaba Bola Tinubu bai bayar da umarni ga wani kamfani na musamman ba wajen aikin.

Umahi ya ce gwamnatin tarayya ta yi aiki cikin gaskiya da riƙon amana wajen tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin saye da samar da ayyuka yadda ya kamata.

By ukarofi