
Daga BELLO A. BABAJI
Biyo bayan cecekuce game da dakatar da ita da zuwanta zaman Majalisar Dokoki ta Duniya a New York, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana yadda ta ɗauki nauyin tafiyarta ba tare da umarnin Majalisar Dattawan Nijeriya ba.
Sanatar ta bayyana hakan ne bayan samu labarin cewa hukumomin tsaro na leƙen asiri suna bincike game da zuwanta zaman, wanda Majalisar Dattawan ta shigar da ƙorafi a kai.
Ta ce, ta yi rajista ne ta yanar gizo wanda ya sa aka amince mata zuwa taron, kamar yadda a baya ma haka aka yi a yayin shirya zaman.
Ta kuma ce, ita ce wadda ta biya wa kanta kuɗin zirga-zirgarta na zuwa wajen da aka tsara zaman, ta na mai cewa dakatar da ita da aka yi bai cire halascinta na zama zaɓaɓɓiyar sanata ba.
Ta ƙara da cewa, tana ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci zaman a shekarar da ta gabata, kuma sunanta ya na cikin jaddawalin Imel, inda ta ce bayan samun damar tafiyar ne sai ta sayi tikitin don halartar zaman.
Har’ilayau, Natasha ta ce halartar zaman ba iyakance shi ga jami’an gwamnati ba kaɗai ba, har da waɗanda aka tantance da ƙungiyoyin al’umma.
A baya ne dai Majalisar Dattawan ta ce ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida tare da soke mata izinin yin wasu ayyuka na musamman har zuwa lokacin da wa’adin zai cika.
