
Daga BELLO A BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da bincike akan yadda Sanatar da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan ta samu halartar zaman majalisar dokoki ta Duniya da aka gudanar a New York ba tare da ayyana ta a matsayin wakiliya ta musamman daga Nijeriya ba.
Majiya daga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce jami’an ƴan sandan farin kaya (DSS) da na Leƙen asiri (NIA) ne suke gudanar da binciken.
Haka kuma hukumomin suna bincike akan wanda ya sahale mata, sannan ko ta halarci taron ne don tozarta Nijeriya.
Majiyar ta ce, Nijeriya ta na ƙoƙarin kiyaye dokokin shiga IPU waɗanda daga ciki dole sai da amincewar ƙasa, kafin wani daga cikinta ya halarci taron da yin jawabi a madadin ta, kamar yadda dokokinta suka shar’anta.
Haka kuma, akwai ƙa’idodin tantancewa idan mutum ya je ƙasar da aka shirya taron waɗanda sai ya bi su kafin a ba shi damar shiga.
Saidai, hukumomin sun ce Natasha ba ta bi waɗannan hanyoyi da aka tsara ba, wadda ta yi bayani game da dakatarwar da aka yi mata daga Majalisar Dattawan Nijeriya.
Ta ce, an siyasantar da batun, wanda ya biyo bayan zargin da ta yi ne na cin zarafi akan Kakakin Majalisar, Godswill Akpabio, da sukar rashin ɗa’a acikin ƴaƴan majalisar.
A nata jawabin, Shugabar IPU Tulia Ackson ta ce sun ji na ɓangarenta, amma ba za su ɗauki mataki ba sai sun saurari ɓangaren Akpabio.
Tun a wajen taron ne, wakiliyar Nijeriya kuma Shugabar kwamitin kula da harkokin mata da ci-gaban al’umma na majalisar dattawan, Kafilat Ogbara, ta yi watsi da zargin Natasha akan Akpabio, inda ta ce an dakatar da ita ne sakamakon rashin kiyaye dokar zama a majalisar.