Dalilin karɓuwar Dattuwa Ali Kumo, inji mazaunin Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Wani mazaunin unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe, Malam Auwalu Ladan, ya bayyana Hon. Hamma Adama Dattuwa Ali Kumo a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin da suka yi fice wajen kusantar jama’a da tallafa musu a lokutan buƙata.

A cewarsa, karɓuwar da Dattuwa Ali Kumo ke samu a tsakanin al’ummar Gombe ba ta ta’allaka ne kawai kan manyan muƙaman da yake riƙe da su ba, illa irin ayyukan alheri da taimakon jama’a da ya daɗe yana gudanarwa.

Dattuwa Ali Kumo, wanda aka fi sani da “Katukan Doma, Sarkin Tafarkin Akko,” na daga cikin fitattun jiga-jigan Jam’iyyar APC a Nijeriya. A halin yanzu yana riƙe da muƙamin Mataimakin Sakataren Kuɗi na APC na ƙasa, sannan kuma shi ne Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Asusun Horar da Ma’aikata na ƙasa (ITF).

Duk da manyan muƙaman da yake riƙe da su, al’umma da dama, musamman a yankin Akko, na bayyana shi a matsayin shugaba mai sauƙin kai da kusanci da talakawa. Mazauna yankin sun ce yana sauraron matsalolin jama’a tare da ƙoƙarin tallafa musu gwargwadon iko.

Auwalu Ladan ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara wa Dattuwa Ali Kumo farin jini shi ne yadda yake ba da muhimmanci ga matasa. Ya ce a lokuta da dama ya tallafa wajen ƙarfafa matasa su rungumi sana’o’i da koyon dabarun dogaro da kai domin rage zaman banza da inganta rayuwarsu.

Haka kuma, an san shi da tallafawa marasa galihu, musamman a lokutan bukukuwan addini da kuma lokacin da jama’a ke fuskantar matsin tattalin arziki. A cewar wasu mazauna yankin, irin waɗannan ayyuka ne suka sa yake samun karɓuwa daga mutane ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko matsayi ba.

Wasu dattawan Akko ma sun bayyana shi a matsayin mutum mai son jama’a wanda ke kasancewa tare da al’umma a lokutan farin ciki da kuma lokacin ƙalubale.

A yau, Dattuwa Ali Kumo na ci gaba da kasancewa cikin shugabannin da ake yabawa saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa rayuwar al’umma da haɗa kan jama’a.

Ga matasa da marasa galihu da dama a Gombe, sunansa ya zama tamkar alamar taimako, kusanci da hidimar jama’a, lamarin da ke ƙara masa karɓuwa da girmamawa a cikin jihar da ma wajenta.

By ukarofi

Leave a Reply