Wata uwa ta zargi jami’an ‘yan sanda da kashe ɗanta, Moses, bayan ya nemi ya yi wa gwamnan Kuros Ribas wa’azi.
Ana zargin ɗan sanda ya hallaka matashin da ya je gidan gwamnan domin yi masa wa’azi da kira zuwa ga Ubangiji.
Mahaifiyar matashin mai suna Moses Mba Onyekachi mai shekaru 23 ta buƙaci adalci game da lamarin.
Ta ce, abin ya faru ne a Kalaba ranar 1 ga Agusta 2025, sun je jana’iza, sai suka samu kira da safe cewa a gaggauta zuwa asibitin sojojin ruwa saboda wata matsala.
Bayan mijinta ya isa wurin, sai ya gano ɗansu aka kai asibiti, suka ce ya nemi yin wa’azi a gidan gwamna Bassey Otu.
Moses ya bayyana cewa Ubangiji ne ya umarce shi ya kai saƙo, amma ‘yan sanda sun hana shi shiga sau biyu, daga ƙarshe sun ɗauki hakan a matsayin barazana.
Bayan haka aka ce an buge shi sannan aka harbe shi, ya kwanta cikin jini tun daga ƙarfe 11 na safe har zuwa bayan rana.
Jami’an Red Cross sun ji harbe-harbe da yamma, sun isa wurin suka tarar da shi cikin yanayi mai muni, aka garzaya da shi asibitin sojojin.
A asibitin an samu jinkiri, suka ce an ba shi kulawar gaggawa domin ya samu ƙarfi da neman sama da N400,000 kafin tiyata.
Daga nan sai ciwon ciki mai tsanani da raunin bugun da ya sha suka karu, daga ƙarshe, ya mutu.
Mun kira wani jami’i, Emmanuel Dickson, wanda ya zo da wasu jami’an tsaro, sai suka fara barin wurin nbayan an tabbatar ya mutu.
Ta ce, a ranar Lahadi an kai gawarsa ɗakin ajiya, aka biya N54,000. Dickson ya yi alƙawarin taimako, amma abin da ya bayar kaɗan ne.
Har ila yau, ta ce washegari jami’an gwamnati da ’yan sanda suka je wajen kwamishinan ’yan sanda da kuma ɗakin ajiya ba tare da yardarsu ba, don duba gawar.
Ta ce, akwai matsala saboda tun farko suna cewa ɗansu yana da tabin hankali, amma sun ƙi amincewa da haka.
