Dangantakar adabi da al’adu

Spread the love

Adabi shi ne ruwan da ke shayar da al’adu – Malam Abubakar Liman

Daga AISHA ASAS

Idan ana magananar adabi mutane na kallonsa a matsayin wata duniya daban da ba ta da alaƙa da al’adun alƙaryar da ke yin sa, wanda ya sa wasu ganin ba ta inda biyun suke da alaƙa.

A ‘yan kwanankin nan na ji wasu suna gardama kan littafan Hausa, wadda wata ta ke masu kallon ababen da ke ɓata tarbiyya tare da gurɓata al’adun Hausa. Ta yi amfani da kalmar “adabin nan ba abinda yake face ɓata al’adunmu.”

Wannan ne ya sa ni tambayar anya ta san me ye ma’anar adabin? Da wannan ne na yi sha’awar faɗar wani abu game da wannan lamarin, saidai mai karatu kada ya yi tunanin ganin rubutu na masana, domin zan ɗan yi tsokaci ne daga cikin ababen da masana ke faɗa.

Kafin mu yi tafiya mai nisa, shin mene ne ake kira adabi?

Kalmar adabi ta samo asali ne daga yaren Larabci, wato dai kalma ce ta aro, kalmar kuwa ita ce adab, wadda za ta iya ɗaukar ma’anar kyautata hali ko ladabi ko ƙwarewa a magana. A ma’ana ta ilimi kuwa, adabi na nufin tarin rubuce-rubucen da suka ƙunshi tunanin ɗan adam cikin salo mai kyau da hikima.

Al’ada kuwa tana nufin ɗabi’u, halaya, dokoki da sauran hanyar rayuwa da al’umma ke gado daga iyaye da kakani.

Adabi da al’ada ‘yan uwan juna ne na jini, wadda ƙarfin ɗaya kan ƙarfafa ɗaya. Idan muka dubi tarihin kowacce al’umma za mu fahimci cewa, adabin ta ne madubin da ke haskaka yadda take rayuwa, yadda take tunani,  da kuma tarin ababen da ta gina rayuwar waɗanda ke rayuwa a ƙarƙashinta da shi na daga tarbiyya da sauransu.

Don haka za mu iya cewa, babu al’ummar da za ta iya tsira da al’adunta idan ba da taimakon adabi ba.

Idan muka yi duba zuwa ga littafin ‘Ruwan Bagaja’ na shahararren marubucin nan Abubakar Imam, ko ‘Magana Jari Ce’, za mu samu cewa, marubutan sun cika rubutunsu da al’adu na Hausawa, tun daga yaren, gaisuwa, zuwa aure, siyasa, cinikayya har ma da yanayin zama da jama’a.

A taƙaice dai za ka ga malam bahaushe a cikin rubutun, wanda kuwa ba ta yadda za ka gane hakan sai ta amfani da al’adun shi na Hausa.

Idan mun koma ɓangaren marubuta irin su Chinua Achebe a ‘Things Fall Apart’, ko Ngugi wa Thiong’o a  littafin ‘The Riɓer Between’, sun yi amfani da adabi wajen kare al’adunsu daga tasirin Turawan mulkin mallaka. 

Wannan na nufin marubucin adabi na ɗaukar al’adunshi a matsayin kayan aikin da tunaninsa zai yi amfani da shi cikin salo na hikima.

A taƙaice dai za mu iya kiran adabi a matsayin madubin da ke haska wa al’adu hanya zuwa ga gyara ko sanar da tarihi da kuma lurarwa cikin hikima, ta hanyar rubutun zube, waƙoƙi da kuma karin magana.

Idan muka ɗauki karin magana a matsayin misali, za mu fahimci cewa, karin magana yana amo ne da irin al’adun da aka yi shi da shi, hakan ke sa karin maganar wasu kan yi wahalar fahimta ga wasu, ba don komai ba sai don bambancin al’adu.

Al’adu suna tsara tunanin marubuci ta hanyar karkata shi zuwa ga abinda yake zahiri gare shi, tun daga yaren zuwa ga ɗabi’u.

Idan muka buga misali da marubucin Hausa, zai iya amfani da tatsuniya wurin gina labari, ko kuma tarihin wani abu da ya shuɗe a ƙasar Hausa wurin ilimantar da al’umma cikin nisahɗi. Haka ma idan ka juya wurin marubutan yamma, za ka tarar suna amfani da ƙa’idojin falsafa da labaran ƙasarsu.

Harshe shi ne gadon al’adu kuma shi ne babban tambari da ake fara bambance al’umma, hakazalika a ɓangaren adabi shi ne jigon sa. Idan marubuci ya bari harshe ya mace, to adabi ne ya mutu, domin da harshen ne zai iya amfani wurin bayyana al’adarsa, har ya kai ga isar da saƙon da ya yi aniyyar isarwa.

Wannan ne ya sa ake auna darajar marubuci da yadda ya ƙware a yaren da yake rubutu kansa. Ta wannan fuska kuwa za mu iya cewa, marubuta sun daɗe suna bayar da gudunmuwa, kasancewar wasu daga cikinsu na amfani da ingantacen harshe wanda wataƙila ma an fara mantawa da shi, ko kuma zuwan zamani ya ɓatar da kalmomin sakamakon amfani da yaren Ingilishi, wanda a wannan zamanin matasa da yawa suke zubar da nasu harshe su riƙe shi gam, wanda hakan zai sa su dinga jani-in-ja-ka da yarensu na gado.

Duk da cewa a wannan zamani da muke ciki marubutan ma ba za su tsira ba, domin da yawa musamman a matasan marubutun sun bi zamani wanda ke shafar al’adunmu da adabinmu.

Wasu marubutun Hausa na rubutu ne da salo na Turanci ko amfani da wasu al’adu na turawa da sunan wayewa, wanda hakan ke kawo sauyi a salo da ɗanɗanon al’adar Hausa. Duk da cewa, wasu masana na ganin haka ba matsala ba ce, a cewarsu al’adu suna canzawa bisa lokaci, kamar yadda adabi ma yake ci gaba da sabuntawa.

Saidai ina ganin idan hakan ta kasance, za a iya wayuwar gari a nemi al’adu a rasa, kasancewar kowacce al’ada a yanzu Turawa ne allon kwaikwayon ta, don haka da yiwar a waye gari duka al’umma suna kamaceceniya ta fuskar al’adu, wanda nake ganin kamar hakan zai iya zama jana’izar al’adu da adabin ta.

A tunani na, idan har marubuta za su tsayu kan al’adu, duk yadda zamani ya canza, idan suka tsayu kan sananiyyar al’ada, to tabbas wannan al’ummar ba zata gushe ba duk tasirin zamani da bin hanyar farar fata.

Al’ada tamkar sutura ce da ke suturta mutum, wanda a duk inda zai shiga zata yi masa rakiya cikin alfahari, matuƙar ya ɗauke ta abin alfahari ɗin. Idan kuwa ba shi da ita, tamkar wanda ke yawo tsirara ne, yana neman inda zai fake kada a ga tsiraicin shi.

Adabi kuwa ba ƙaramar rawa ya taka ba wurin sanar da duniya al’adu da kuma siyan daraja ga al’ummar wurin. Adabi kan taimaka matuƙa wurin sanar da duniya matakin da al’umma ke ciki, kuma yana taimko wurin isar da kukan al’umma idan suna da, ko canza kallon da duniya ke yiwa al’umma.

By ukarofi