Daudu ya buƙaci Nijeriya ta mara wa Amina Mohammed baya a matsayin ‘yar takarar Sakatare Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Wani ƙwararren masani ɗan Nijeriya, Dr. Ibrahim Jalo Daudu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ayyana Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), Amina Mohammed, a matsayin ‘yar takarar Najeriya domin kujerar Sakatare Janar na Majalisar, bayan kammala wa’adin Antonio Guterres na biyu a watan Janairun 2027.

Da yake magana kan sauyin shugabanci da ke tafe a Majalisar Ɗinkin Duniya, Daudu ya bayyana Amina Mohammed a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka fi cancanta, yana mai nuni da gogewarta mai yawa a fannonin bunƙasa ci gaba, harkokin diflomasiyya da gudanar da ayyukan gwamnati.

Ya ce Amina Mohammed ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara ajandar cigaba mai ɗorewa ta 2030 da kuma manufofin cigaba mai ɗorewa (SDGs) a lokacin da take mai ba tsohon Sakatare Janar na MƊD, Ban Ki-moon, shawara ta musamman.

Daudu ya ƙara da cewa tun bayan naɗinta a matsayin mataimakiyar Sakatare Janar a shekarar 2017, Amina Mohammed ta jagoranci ƙoƙarin bunƙasa cigaba mai ɗorewa, yaƙi da sauyin yanayi, ayyukan jin ƙai da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen duniya.

Daudu, wanda ke riƙe da sarautar Tafarkin Gombe, ya kuma bayyana irin gudunmawar da Amina Mohammed ta bayar a Najeriya, inda ya ce ta yi aiki a gwamnatocin tsoffin shugabannin ƙasa Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari, inda ta taka rawa a shirye-shiryen rage talauci, kare muhalli da manufofin sauyin yanayi.

Ya kuma tunatar da cewa Amina Mohammed ce ta jagoranci kwamitin karɓar mulki na Jihar Gombe a shekarar 2019 bayan zaɓen Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

A cewarsa, tarihin aikinta ya nuna ƙwarewa, nagarta da jajircewa wajen yi wa jama’a hidima, abin da ya sa ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi dacewa da jagorantar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ya buƙaci Najeriya ta haɗa kai wajen mara mata baya, yana cewa:

“Amina Mohammed ta wakilci Najeriya cikin kima da mutunci, kuma tana da gogewa da amincewar duniya da suka cancanci ta jagoranci Majalisar Ɗinkin Duniya. Ya kamata Najeriya ta haɗa kai ta mara wa ɗaya daga cikin fitattun ‘ya’yanta mata baya domin zama Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya.”

By ukarofi

Leave a Reply