Davido da Chioma: Auren farko ko na biyu?

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Duk wani da zai iya iƙirarin ya san muhimman abubuwa game da shahararren mawaƙi David Adeleke, wanda mutane suka fi sani da Davido, tabbas zai san ko wacce ce Chioma Avril Rowland a rayuwar mawaƙin, kasancewar irin soyayyar da yake bayyana wa duniya yana yi mata, ciki kuwa har da waƙa da ya yi da ke ɗauke da matsayin masoyiyar tasa Chioma. 

Sai dai abinda da yawa daga cikin masoyan mawaƙin ba su sani ba shi ne, auren mawaƙin wanda ya gudana a ranar Talatar da ta gabata, bai zama ranar auren mawaƙin da masoyiyarsa na farko ba, saidai za mu iya kiransa da aure na farko da aka yi a bayyane. 

A watan Maris na shekarar 2023, Davido ya sanar a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da sakin kudin waƙarsa na ‘Timelss’, cewa ai tuni sun yi auri Chioma.

A cewarsa, sun yi auren ne a lokacin da ya dakatar da waƙoƙi domin makokin ɗansa na farko Ifeanyi, wanda ya rasu a Nuwamban 2022 ta hanyar faɗawa ruwa.

Wannan lamarin bai zama abin mamaki ba duba da cewa, soyayyar Davido da Chioma an jima ana yin ta, kuma tun lokacin da ta ke da cikin ɗansa na farko da ya rasu ya gabatar da niyyar aurenta inda aka yi musu baiko a Satumban 2019. Sai dai abubuwa sun sauya lokacin da yaron ke shekara guda a duniya.

A kowacce alaƙa ta rayuwa akan samu irin wannan matsaloli musamman ma a zancen soyayya, sau da yawa za ka iya tarar da masoyan da suka jima tare kamar ba za su iya rabuwa ba, amma rana tsaka ka nemi kyakkyawar soyayyar tasu ka rasa. Saidai za mu iya cewa a ɓangaren mawaƙi Davido da Chioma ta bambanta, dalilin namijin ƙoƙarin da suka yi wurin ganin duk matsalolin da suke fuskanta ba su hana su kasancewa tare ba, ma’ana dai a kowane lokaci sukan lalabe hanyar dawowa ga juna bayan kowane saɓani da za su samu.

By ukarofi