DCP Abba Kyari ya maka Gwamnatin Tarayya a kotu

Daga BASHIR ISAH

DCP Abba Kyari wanda yake tsare a hannun hukumar NDLEA bisa zargin fataucin miyagun ƙwayoyi, ya maka Gwamnatin Tarayya a kotu a ranar Litinin.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, cikin ƙararsa da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, Kyari ya buƙaci kotu da ta talista wa Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) kan ta bada belin shi saboda dalilai na kula da lafiyarsa kafin lokacin da za a saurari shari’arsu.

Cikin takardar da ya tura wa kotu ta hannun lauyarsa, Mrs. P. O. Ikenna, Kayari ya shaida wa kotu cewa ana tsare da shi ne bisa zargi na ƙarya da ƙaƙaba masa.

Da alama dai haƙƙar Kyari ta neman beli ba ta cimma ruwa ba, don kuwa Aƙali Ekwo ya ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga Fabrairu, tare da bada umarin a tabbatar da duka takardun da suka dace sun isa ga Gwamnatin Tarayya.

Kyari ya faɗa a komar NDLEA ne tun bayan hukumar ta bankaɗo wata harƙallar safarar miyagun ƙwayoyi wanda ake zargin da hannunsa ciki dumu-dumu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *