Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Kungiyar Gamayyar Al’ummar Arewacin Nijeriya wacce ake yi wa taken ‘CNG’ da laƙabin ‘Coalition of Northern Groups’ ta ƙalubalanci mambobin majalisun dokoki na tarayya da cewar, duk waɗanda suka ƙi bayar da gudunmawar da ta dace domin yin fatali da dukkan tanade-tanaden son zuciya dake ƙunshe cikin waɗannan dokoki na tattara haraji da Shugaban ƙasa ya ƙirƙiro, su kwana da sanin sun zalunci kansu, sun zalunci Nijeriya da kuma mutanen Nijeriya.
“Haka-zalika, duk mambobin majalisar dokokin tarayyar Nijeriya da suka dage, suka tashi, suka cimma bincika waɗannan dokoki daga inda nasarorin gwamnoni jihohi suka tsaya, suka tashi suka ɗora, su kwana da cewar, sun taimaki kawukansu, sun taimaki Nijeriya da ɗaukacin mutanen Nijeriya”
Kodinetan ƙasa na wannan ƙungiya, Kwamred Jamilu Aliyu Charanchi a cikin wata ganawa da ƙungiyar tayi da manema labarai a garin Bauchi yace, babu wani dalili a wannan lokaci da al’umma take ɗanɗana wahalhalun rayuwa dabam dabam, ace za’a ƙara kuɗaɗen haraji, yana mai cewar wannan ƙuduri na gwamnati, zalumci ne da ake nufin yi domin daɗaɗa wa wani maluki, gungun, ko biyan wata bukata ta son zuciya.
“Kuma yaya ma za’a ce saboda Bola Ahmed Tinubu domin tun lokacin da yayi Gwamnan Legas zuwa yau tattalin arzikin wancan jiha take hannun sa, Kuma sai abinda yake nufi za’a aiwatar a Legas, ace sai yayi wa Nijeriya makamancin wancan mulkin, ‘yan Nijeriya ala-tilas su kasance bayi?
“Domin akwai kuma wata jita-jita mai ƙarfi ta kawo wata hukuma wacce bata gwamnati bace da zata riƙa tattara haraji a ɗaukacin faɗin Nijeriya, da za’a riƙa yi mata tagomashin kashi 13 cikin 100 daga kuɗaɗen data tattara mallakin ta, tamkar batun gaso rogo a baka ɓawo. Wannan zalunci ne da yake neman mayar da ‘ya’yan Nijeriya shanun tatsa, ba zamu amince da hakan ba, kuma zamu cigaba da tirka-tirkan daƙushe wannan manufa ta baba-kere”, a cewar Charanchi
ƙungiyar, ta kuma sake jan kunnen rashin yarda da cire haraji daga cikin kuɗaɗen gado na mamaci, tana mai cewar, yin hakan yayi saɓani ko banbaraƙwai da tanade-tanaden addinin musulumci, kuma tantagaryar zalumci ne wa magada ko masu gado.
Kwamared Jamilu Charanchi ya kuma ce sam ba daidai bane ace hukumomin gwamnati da suke tattara haraji, kamar kostom, masana’antar fetur da sauran su, ace za’a shaƙe masu gudanar da waɗannan aiyuka na tattara kuɗaɗen haraji, a ƙirƙiro wata hukuma mallakar wani mutum mai hannu da shuni ko riƙe da kujerar milki, ace itace zata ke tattara dukkan kuɗaɗen haraji, ana bata lada na kashi 13 cikin na dukkan kuɗaɗe data tara.
Charanchi ya ƙara da cewar, kuma ba daidai bane ace za’a hanawa hukumomi masu yin tallafi kuɗaɗen gudanar da aiyukan su, kamar hukumar ‘TETFund, NITDA, NASENI’ da makamantan su. Waɗannan hukumomi suna da muhimmanci wajen ciyar da ilmi gaba, bunkasa harƙoƙin ƙere-ƙere, kimiyya da fasaha, don haka, duk wani yunƙuri da za’a yi domin gurgunta waɗannan hukumomi, ba su yarda da hakan ba, arewa bata yarda da hakan ba, kuma bata amince ba.
“Wannan ƙungiya ta gamayyar arewacin Nijeriya tana bisa ɗudurin ta na zage damtse domin tabbatar da cewa, dukkan wani lamari da bai yiwa al’umma daidai ba, duk abu da zai cuci al’ummar Nijeriya, dukkan wani abu da zai ƙarawa al’umma wahala, zamu yaƙe shi kamar yadda doka ta tanadar. Idan Allah ya yarda, babu gudu, babu ja da baya, kuma wannan ƙungiya tana yine domin al’umma, domin yankin arewa, kuma domin ƙasar Nijeriya.”
Gwamnoni ba mu ce ba mu yaba ba, mun yaba ƙwarai da gaske, kuma ai karo na farko ne da gwamnan APC, gwamnan PDP, gwamnan kowace jamiyya suka haɗu guri guda suka ce, bamu yarda da wannan abu ba. Koda ana ganin su suna da moriya a cikin lamarin, gobe idan akace za a yi zaɓe, babu yadda za’a yi wani gwamna mai almundahana ko ra’ayin koma-baya ya sake dawowa bisa karagar mulki.
“Gwamnoni sun yi iyakar tasu iyawar, kuma muna jinjina masu akan nasu ƙoƙarin, amma bai isa ba, shi yasa muke kira ga ‘yan majalisa waɗanda waɗannan dokokin yin gyara wa tsarin tattara haraji yake gabansu, su kwana da sanin cewa har ya zuwa yau, babu wata jami’a ko makaranta da ake yin karatu mai zurfi da ta goyi bayan a rushe, takura, ko hana hukumar Tetfund kuɗi da nufin rage mata ayyukan da take yi na tallafi. A ƙasar nan, babu inda ba za ka ga ayyukan TETFund ba, walau jami’a ce ko kwaleji, ko ma’aikatar ilimi walau a matakin tarayya ko ta jiha, saboda haka, hanawa TETFund gudanar da ayyukan tallafi wani babban zalunci ne ga al’umma,” inji CNG.
