Dokar ta-ɓaci: Tinubu ya gana da Fubara kan rikicin siyasar Ribas a karon farko

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Nujeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da aka dakatar, a wata ganawa ta musamman da ta gudana a birnin Landan.

Ganawar ta biyo bayan dogon rikicin siyasa ne da ya dabaibaye jihar wanda ya kai ga sanya dokar ta-ɓaci.

An tabbatar da cewa Fubara ne ya nemi ganawar, inda suka tattauna batutuwa da dama da suka shafi makomar siyasar jihar.

Wannan ita ce ganawa ta farko tun bayan da Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas ranar 18 ga Maris, ya kuma sauke Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, daga muƙamansu. 

Rahotanni daga fadar shugaban ƙasa sun nuna cewa ganawar ta fi karkata ne wajen nemo mafita ga halin da jihar Ribas ke ciki.

Wannan na zuwa ne bayan da shugaba Tinubu ya jaddada cewa rikicin siyasar jihar ya zama barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi, inda ya ce rikicin ya hana gudanar da gwamnati yadda ya kamata.

Ya naɗa tsohon Hafsun Tundunar Sojan Ruwa, Ibok-Ete Ekwe Ibas, a matsayin shugaba mai riƙon ƙwarya a jihar.

Sai dai gwamnoni daga jihohin PDP sun kai ƙara Kotun ƙoli domin ƙalubalantar wannan mataki na shugaban ƙasa, suna neman dawo da doka da tsarin mulki. 

Koda yake ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna ba, wasu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun ce ana duba yiwuwar dawo da Fubara ofis kafin wa’adin wata shida ya cika.

Majiyoyin sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar, kuma yanzu ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, bai halarci ganawar ba.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Nyesom Wike bai ji daɗin ganawar da aka yi tsakanin Tinubu da Fubara ba tare da saninsa ba. 

Ana sa ran Tinubu zai gudanar da wata ganawa nan gaba da Fubara, Wike da ‘yan majalisar dokokin jihar domin samar da mafita da za ta dawo da zaman lafiya a jihar Ribas.

By ukarofi