Dole mu ba matasa dama a siyasar 2027 – Bafarawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa, wanda a kwanakin baya ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP, ya ce dole tsofaffin ‘yan siyasa tsararrakinsa su kauce, su ba matasa wuri a siyasar 2027.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Blueprint, Bafarawa ya ce, “ba rikici nake yi da PDP ba. Mutane suna kuskuren tunanin dole ɗan siyasa ya nemi takarar zama zaɓaɓɓe, amma siyasa ta wuce haka, siyasa magana ce da hidimtawa al’umma.

“Na yi kusan shekara 48 a siyasa, amma yanzu na kai shekara 70 a duniya. Aikin da ke gabana ya wuce maganar Sakkwato, yanzu tunanina shi ne, yadda zan inganta Nijeriya, musamman yankin Arewa.”

Ya ce wannan ne ya sa ya kafa ƙungiyar Northern Star Youth Alliance, “za mu haɗa hannu da Musulmi da Kirista domin mu samu nasara.”

Ya ce zai iya goyon bayan ɗantakara ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ba, inda ya ƙara da cewa dole su ba matasa wuri a siyasar da ke tafe, domin a cewarsa, “dole mu jawo su domin mu ba su dama su gwada. Kun ga ai Janar Yakubu Gowon ma ya zama shugaban ƙasa ne yana ɗan shekara 30.”

By ukarofi