Dole ‘yan siyasa su soma yin rigakafin korona kafin talakawa su bi sawunsu, inji Sultan

Daga UMAR M. GOMBE

Mai Girma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su fito baina jama’a su yi allurar rigakafin cutar korona na AstraZeneca domin hakan ya zama ƙarfafawa da ƙwarin gwiwa ga sauran jama’a.

Sarkin ya yi wannan kira ne yayin wani taron wayar da kai da aka shirya game da rigakafin cutar korona ga Musulmi a Juma’ar da ta gabata don faɗakar da malamai da kuma limamai.

Basaraken ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su je su yi allurar saboda a cewarsa, ta dalilin rigakafi ne Nijeriyar ta samu nasarar kuɓuta daga cutar poliyo kimanin shekaru goma da suka gabata.

Ya ce, “Mun ga yadda Shugaban Ƙasa ya yi tasa allurar a bayyane, haka muke sa ran su ma shugabannin siyasa su yi tasu a bayyane.

“Mun yi ammanar cewa dole ɗaukacin shugabannin siyasa su shige gaba wajen soma yin rigakafin kafin talakawa su bi sawunsu saboda su ne shugabanninmu.

“Akwai mutane da dama waɗanda ba su yarda da allurar rigakafin cutar korona ba, ko kuma gaskiyar ita kanta cutar, amma mu mun yarda akwai cutar saboda ta yi ajalin wasu abokai da kuma ‘yan’uwamu.

“Yana da matuƙar muhimmanci wayar da kan jama’a kan cewa lallai wannan cuta akwai ta kuma akwai yiwuwar a rabu da ita. Amma ya rage gare ku ne ku ɗauki matakin da ya dace.

“Ra’ayin yin rigakafin ya rage naku, don kuwa ba za mu tilasta ku a kan haka ba. Sai dai muna kira a gare ku kamar yadda muka yi muku a lokacin rigakafin poliyo wadda a dalilin haka a yau ga shi an shawo kanta (poliyo).

“Muna sane da irin rawar da kuka taka, maganganunku suna da tasiri kuma jama’a na sauraron ku kuma sun yarda da ku.”

Kawo yanzu, kimanin allurar rigakafin korona sama da dubu takwas ne aka yi wa ‘yan Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *