Ogun: ‘Yan bindiga sun sace Sarkin Ijebu-Igbo

Daga WAKILINMU

Rahotanni daga yankin Ijebu-Igbo a jihar Ogun sun nuna wasu ‘yan bindiga sun sace sarkin yankin, Oba Alade Meta, a ranar Asabar.

Wata majiya ta ce a wannan rana, sarkin ya bar fadarsa da misalin ƙarfe 11 da wata motarsa ‘jeep’ zuwa unguwa. A kan hanyarsa ta komawa gida misalin ƙarfe 3 na rana, ‘yan bindiga suka tare shi a hanya, suka fidda shi a motarsa tare da yin awon gaba da shi sanna suka bar motar tasa a nan.

Tun daga wannan lokaci ya zuwa haɗa wannan labari, babu wanda ya san inda sarkin yake. Haka ma ‘yan sandan yankin ba su kai ga tabbatar da faruwar lamarin ba.