Dorinar ruwa ta yi ajalin dogarin Sarkin Yawuri

Spread the love

An shiga firgici bayan da wata dorinar ruwa ta yi ajalin dogarin Sarkin Yawuri da ke Jihar Kebbi.

Marigayin, mai suna Usman Maigadi, ya rasa ransa ne a cikin lambun Mai Martaba Sarkin Yawuri, Alhaji (Dr.) Muhammad Zayyanu-Abdullahi.

An ruwaito cewa dabbar ta yi tsammanin marigayin na ƙoƙarin zuwa inda ta ke domin cutar da jaririyarta ne.

Rahotannin sun tabbatar da cewa marigayin mai shekaru 60 ya gamu da tsautsayin ne a ranar Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tillo da ke ƙaramar Hukumar Yauri yayin da dattijon ke kamun kifi.

Shugaban ƙaramar Hikumar Yauri, Alhaji Abubakar Shu’aibu ya ce an binne marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Tuni aka gudanar da sallar jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar” inji Abubakar Shu’aibu.

Gwamna Nasir Idris na jihar Kebi ya nuna alhini kan rasuwar marigayin a ƙaramar hukumar Yauri.

Sanarwar na ƙunshe ne a cikin wasiƙar da hadiminsa, Alhaji Ahmed Idris ya fitar game da tsautsayin.

Sanarwar ta ce, Gwamna Nasir Idris ya kaɗu da lamarin inda ya tura saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin da kuma masarautar Yawuri.

By ukarofi