‘Downloading’: Kace-nace ya ɓarke tsakanin Hisbah da hukumar tace finafinan Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Hukumar Tace Fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano (KSFCB) ta ce, har yanzu ba ta soke ko ta haramta sana’ar ‘downloading’ a faɗin jihar ba. Hukumar ta bayyana haka ne bayan ta ce, ta samu koke-koke daga masu wannan sana’a da shugabanninsu kan rahotannin da ke yawo cewa an hana gudanar da sana’ar tura finafinai a waya a faɗin jihar.

Idan za a iya tunawa, a jiya ne aka ji wani saƙon murya da ake danganta shi da Mataimakin Kwamandan Hisbah, wanda ke bayar da umarnin haramta sana’ar ‘downloading’ a faɗin jihar bakiɗaya.

A cikin wata sanarwa, hukumar tace finafinan ta ce, babu wata hukuma da ta tuntuɓe ta ko ta yi shawara da ita kafin a yaɗa irin waɗannan bayanai. Ta ce, masu sana’ar ‘downloading’ na daga cikin waɗanda take da alhakin sa ido akan ayyukansu bisa dokar da ta kafa hukumar tare da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu ya karya ƙa’idojin gudanar da sana’ar.

Ta kuma ce, ba ta karɓi wani ƙorafi a hukumance ba dangane da lamarin. Sai dai ta ce ta gano wani saƙon murya da yake yawo a shafukan sada zumunta, wanda ake zargin wasu masu ‘downloading’ da yaɗa bidiyoyin tsiraici.

A cewar sanarwar da kakakin hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya ce, binciken matakin farko ya nuna cewa, ana zargin muryar da ke cikin saƙon ba daga Jihar Kano take ba, amma hukumar ta ce tana ci gaba da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru. Hukumar ta ce, ta tura jami’anta a ƙananan hukumomi 44 na jihar tare da Babban Kwamitin Sa Ido domin binciken masu yaɗa saƙonni da hotunan da ake zargin sun saɓa wa doka da tarbiyya. Ta ƙara da cewa, har yanzu ba a gano waɗanda ake zargi ba, amma ana ci gaba bincike.

Game da matsayarta kan sana’ar tura finafinai a waya, hukumar ta ce ta yi la’akari da yarjejeniyoyin kasuwanci da wasu masu sana’ar suka ƙulla da masana’antar Kannywood wajen rarrabawa da dillancin fina-finai. Ta ce, bayan nazari, ta yanke shawarar ci gaba da ba matasa damar gudanar da sana’ar, saboda muhimmancinta wajen samar da abin dogaro da kai da bunƙasa tattalin arziki.

Sai dai hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai kan duk wanda aka samu yana amfani da sana’ar wajen yaɗa abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya ko koyarwar addinin Musulunci.

A ƙarshe, hukumar ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin gwamnati, shugabannin ƙungiyar masu downloading da sauran al’umma domin magance duk wani abu da zai iya bata sunan sana’ar, tare da buɗe ƙofarta ga duk wanda ke da sahihan bayanai da za su taimaka wajen tabbatar da bin doka da oda.

Hukumar ta bayyana matsayarta ne bayan da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta haramta gudanar da sana’ar ta downloading a Kano. Mataimakin kwamandan Hisbah na jihar Kano Dr. Mujahid Aminudeen ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aikawa manema labarai. Ya ce, sun dauki matakin ne domin kare tarbiyya matasa dake neman lalacewa, sakamakon yadda masu downloading ɗin suke turawa matasa fina-finan batsa.

Sannan ya kuma ce hukuma ba za ta lamunci duk wani abu da zai lalata tarbiyya matasa a jihar Kano ba, ya ce hakan ce ma tasa suka baza jami’ansu a dukkanin kananan hukumomi 44 dake Kano domin Kamo masu kunnen kashi domin gurfanar da su a gaban kotu don su girbi abun da suka shuka.

Sanarwar ta KSFCB ta tayar ƙura, saboda cin karo da ta yi da wancan umarni da aka danganta shi da Hisbah.

By ukarofi

Leave a Reply