DSS ta miƙa wa Buhari rahoton sabbin zarge-zarge 12 kan Emefiele

*Tana zarginsa da karkatar da tallafin IMF biliyan N3.6 na korona

Daga WAKILINMU

Har yanzu dai Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, bai ga ta zama ba a wusan buyar da yake yi tsakaninsa da hukunar DSS.

Domin kuwa, a ranar Alhamis DSS ta sake miƙa ƙarin hujjoji ƙwarara ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari dangane da sabbin zarge-zargen almundahanar da ta bankaɗo a kan Emefiele.

Jaridar First News ta kalato Darakta-Janar na DSS, Yusuf Bichi, da kansa ya miƙa wa Buhari hujjojin a Fadar Shugaban da ke Abuja.

Majiyarmu ta ce samun wannan rahoto daga DSS ya sa Buhari ya gayyaci Emefiele ɗin a ranar Alhamis, wanda hakan ya sa shugaban CBN ɗin ganawa da Buhari sau biyu a wannan rana.

Sabbin zarge-zargen na DSS na zuwa ne bayan da Emefiele ya buƙaci jami’an DSS da ke ba shi tsaro da su janye su koma ofishinsu a ranar Larabar da ta gabata.

Lamarin da aka ce ba ya rasa nasaba da girke dakarun soji da Shugaban Tsaro, Janar Lucky Irabor, ya yi a hedikwatar CBN tare ba su umarnin karɓe ragamar tsaron bankin da na iyalan Emefiele.

An yi zargin Irabor ya samu kuɗi kimanin biliyan N1 a wajen Emefiele domin ba shi kariyar da za ta hana DSS cafke shi.

A cewar DSS binciken farko ya gano Emefiele na da hannu a badaƙalar wawurar kuɗaɗe da dama kuma a wurare daban-daban.

Ammam Emefiele ya ci gaba da neman duk wata hanyar da za ta ba shi damar kuɓuta daga barazanar DSS, daga ciki har da jinkirin dawowa daga hutun da ya tafi a ƙetare.

Majiyarmu ta ce, Mamman Daura da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, na daga cikin shafaffu da man da ke matsa wa shugaban DSS lamba kan ya ƙyale Emefiele, wanda hakan ne sanadiyar DSS ta kasa tsare Emefiele ɗin a baya.

Yayin binciken da ta gudanar a lokacin da Emefiele ke hutu, DSS ta bankaɗo sabbin zarge-zarge guda 12 a kan Emefiele kamar yadda First News ta rawaito.

Daga cikin zarge-zargen, DSS ta gano Ministar Kuɗi ta amince an fitar da kuɗin da ya kai tiriliyan N23.7 saɓanin tiriliyan N7.3 da aka gabatar wa Majalisar Tarayya.

Akwai kuma zargin karkatar da biliyan N3.6 a matsayin kuɗin rage raɗaɗin Korona da da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bai wa Nijeriya shekaru biyu da suka gabata.

Cewa Emefiele ya yi biris ba tare da sanar da Gwamnatin Tarayya batun tallafin na IMF ɗin ba, sannan ya karkatar da kuɗin zuwa wani asusu na daban a ƙasar Chana.

Asiri ya fallasa ne bayan da IMF ya buƙaci Ministar Kuɗi ta ba shi shaidar karɓar kuɗaɗen, wanda aka ce Emefiele ya faɗa wa Ministar cewa ya zuba wa Nijeriya jari da kuɗin, da dai sauransu.