AFCON 2025: George Weah ya juya wa Nijeriya baya duk da ziyarar da Osinbajo ya kai ma sa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasar Laberiya, George Weah, ya ƙara nuna goyan bayansa ga yunƙurin Makoro na karɓar baƙuncin gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 (AFCON).

Tsohon ɗan wasan wanda shi ne ɗan Afirka ɗaya tilo da ya taɓa lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa ta Ballon d’Or, da ake bai wa gwarzon ɗan wasan duniya, ya ce, ya nuna cikakken goyon bayansa ga ƙasar da ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar kofin duniya na Qatar 2022.

Wannan na zuwa ne sa’o’i 72 bayan mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya ziyarci ƙasar Laberiya domin halartar wani taro mai taken, “Tattaunawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa da Matasa,” wanda takwaransa na Laberiya, Dokta Jewel Howard-Taylor ke shiryawa, a wani ɓangare na ayyukan bikin cikar Howard Taylor shekaru 60 da haihuwa.

Wata sanarwar manema labarai da mai taimaka wa mataimakin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Mista Laolu Akande ya fitar, ta ce Osinbajo zai kuma gana da shugaban ƙasar Laberiya, George Weah.

Osinbajo da wasu shugabanni daga yammacin Afirka sun yi mu’amala da wasu zaɓaɓɓun shugabanni ƙasashe 400 masu tasowa inda su ke raba ci gabansu, gwagwarmaya, nasarori da kuma sirrinsu, a cewar bayanai daga ofishin mataimakin shugaban ƙasar Laberiya.

Tabbas Osinbajo ya nemi goyon bayan Weah kan neman haɗin gwiwar Nijeriya da Benin a gasar AFCON na 2025, amma daga baya Weah ya nuna goyon bayansa na neman Maroko ta baƙunci wasa sa’o’i 72 bayan ziyarar Osinbajo.

Weah ya bayyana goyan bayansa ne a cikin wani rahoto na Medays International Peace Forum da aka aika zuwa Maroko wanda News Point Nigeria ta samu a ranar Juma’a. An shirya taron zaman lafiya a birnin Tangier na Morocco, a watan Nuwamba 2022.

Weah ya ba da misali da zuba jarin da Moroko ke yi a fagen bunƙasa ƙwallon ƙafa, ya kuma ce tuni ya fara yaƙin neman zaɓen tare da masu ruwa da tsaki a nahiyar.

Ɗan wasan mai shekaru 56, wanda ya buga wasa a ƙungiyoyi da suka haɗa da Monaco da AC Milan da Chelsea a tsawon shekaru 18, ya kuma yi magana game da yadda Maroko ta kawo babban abin alfahari a Afirka a lokacin gasar cin kofin duniya.