DSS ta rufe ofishin kakakin majalisa da na mataimakinta a Legas

Daga BELLO A. BABAJI

A safiyar ranar Litinin ne jami’an tsaro na DSS da haɗin-gwiwar ƴan sanda suka kai samame a Majalisar Dokokin Jihar Legas, inda suka rufe ofishin Kakakinta, Mojisola Meranda da na mataimakinta da kuma na Akawon majalisar.

Zuwa ƙarfe 10 na safe ne jami’an tsaron suka karɓe iko da zauren Majalisar wanda ke Alausa a Ikeja, babban birnin jihar.

Daga nan sai suka yi ta musguna wa waɗanda ke wucewa ta kewayen majalisar, inda da misalin ƙarfe 11:15 ne kakakin ta isa da tawagarta.

A tare da ita, mambobi 32 na majalisar ne suka halarci zaman a lokacin da jami’an suka isa, inda suka zagaye farfajiyar majalisar da motocin tsaro.

A watan da ya gabata ne ƴaƴan majalisar suka tsige toshon kakakin majalisar, Mudashiru Obasa bisa zargin sa da hannu a badaƙala da wasu ayyukan da suka saɓa wa doka.