
Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), ta ce ta kori wasu jami’anta su guda 115 daga aiki, saboda abinda ta kira da ‘wasu sauye-sauye da take yi’.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, DSS ta shawarci al’umma da su kauce wa mu’amala da jami’an a matsayin wakilan hukumar.
Bayanan mutanen da hukumar ta fitar sun nuna cewa an kori mutanen ne tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025.
Hakan na zuwa ne bayan da a watan Oktoban da ya gabata hukumar ta kama wasu tsofaffin jami’anta biyu bisa zargin su da amfani da sunan hukumar suna damfarar mutane.
Hukumar ta kuma wallafa sunaye da hotonan jami’an da ta ce ta koran a shafinta intanet kamar yadda za a gan su a ƙasa.




