Dujiman Katsina ya jinjina wa hukumar Civil Defence a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin hukumomin tsaron cikin gida na majalisar wakilai Hon Abdullahi Aliyu ya yabawa babban kwamanda na hukumar Civil Defence ta ƙasa Abubakar Audi bisa ƙoƙarin da yayi na sake fasalin hukumar.

Ɗan majalisar wakilan ya yi wannan yabon ne a Katsina yayin da yake liƙa wa shugaban sashin koda ta kwana na hukumar a Katsina CS Jibiril Usman.

Hon Abdullahi Aliyu kuma Dujiman Katsina ya ƙara bayyana cewa sabbin tsare tsare da kwamandan ya fito da shi zai taimaka gaya wajen kare muhimman kadarorin gwamnati da magance masu ma gwamnati zangon ƙasa.

Ya kuma taya babban sufeto Jibril Usman murna akan ƙarin girma da ya samu wanda yace abin bai bashi mamaki ba ganin yada shi Usman ya sadaukar da kan sa da jajircewa a wajen aiki tsawon shekaru 14 da fara aiki.

CS Usman shi ke lura da sashin kula da manyan baƙi da kuma sashin shirya tsare tsare na yadda hukumar za ta tabbatar da tsaro a jihar. Kuma ƙwararre ne wajen yaƙi da ta’adanci da kuma safarar makamai.