Tare da ALI ABUBAKAR SADIQ
Tun a zamanin Shagari aka fara maganar aikin madatsar wutar lantarki ta Mambila, amma abin bai yiwu ba. Obasanjo, a lokacin mulkinsa ya dawo da maganar ya kamata a yi wannan madatsa ta Mambila a kan kogin Donga na Jihar Taraba. An ce har kusan Dala miliyan 350 aka ware, domin yin nazarin yanayi (feasibility studies). Amma dai shi ma har Obasanjo ya bar mulki babu abinda aka yi.
Zuwan Jonathan, a ƙoƙarinsa na jan hankalin ’yan Arewa, ya sa an ɗauko wannan nazarin yanayin (feasibility studies) kuma an fara zawarcin waɗanda za su gina wannan tashar wutar lantarki ta Mambila. Daga baya an cimma yarjejeniya da wani kamfani na China zai gina madatsar wutar lantarkin ta Mambila a kan Dala biliyan 32.
Aikin dai bai yiwu ba har zuwan Buhari. Mutane da dama sun kama murna lokacin da Buhari ya ce, aikin da zai sa a gaba shine na Mambila. Kuma a wani yunƙuri mai ban mamaki da burgewa shine kafin ka ce me, an janyo katafaren kamfanin CCCEC na China, wanda ya gina dam mafi girma a tarihin duniya, wato 3 Gorges Dam da ke China.
Wannan kamfani da haɗin gwiwar bankin harkokin ƙasashen waje na China, sun yarda za su gina wannan madatsar lantarki ta Mambila a kan kuɗaɗe Dala biliyan 5.7 kacal. ƙwarai kacal mana idan muka yi la’akari da cewa, an ceto wa Najeriya kimanin Dala biliyan 27 daga tsohuwar kwangilar Jonathan a kan wannan aiki ta Dala biliyan 32.
Giɗi-giɗi aka kama abubuwa kamar gaske, aka jawo masana da ƙwararru aka fara tattaunawa. Wasu matsiyata suka zugo wani kamfani ya shigar da ƙarar Gwamnatin Tarayya kan cewa, an ƙwace tsohuwar kwangilar ba tare da cika wasu sharuɗɗa ba. Wannan lamari ya kawo tsaiko. Daga baya aka ce a je a sasanta, inda wancan kamfani ya nemi a ba shi Dala miliyan 200.
Ba a taɓa fito da wani aiki a tarihin Arewacin Najeriya da ya kai mahimmancin na Mambila ba, domin baya ga wutar lantarki da zai samar kimanin megawatts 3050, aiki ne da zai kawo haɓakar tattalin arziki na Arewa maso-gabas, Arewa kanta da Najeriya bakiɗaya.
Ko kun san cewa, wannan aiki, idan kamfanin Ajaokuta na aiki ba tsayawa, Madatsar Mambila za ta laƙume duk ilahirin ƙarfen da za ta samar na shekara guda? Dangote da Bua da Ashaka za su yi watanni su na kai sumunti wajen? An fara tsarin yadda za a koyar da dubban matasa ayyukan walda, kafinta, lebura da sauran sana’o’i? Za a gina sabon gari, domin tsugunar da waɗanda za a tasa? Za a gina sabuwar tashar saukar jiragen sama a Taraba tare da gina sabbin otel? Har wani kamfani ya fara shirin aikin safarar mutane daga Abuja zuwa filin aikin a jirgi mai saukar ungulu (helicopter serɓices). Za a gina sabbin titina, hatta kamfanin Fiat Trucks na Kano ana sa ran farfaɗowarsa ta hanyar samar da motocin aiki a Mambila.
Kai abin fa Allah kaɗai ya san waɗanda za su ci abinci sakamakon wannan aiki. Abin takaici mafi muni shine ba a taɓa bijiro da aiki mai araha da sauƙi irinsa ba, domin a cikin kuɗin aikin na Dala biliyan 5.7, Bankin China zai samar da Dala biliyan 4.845, kaso 85% na aiki yayin da Nijeriya za ta samar da Dala miliyan 855 ne kacal, wato kaso 15%. Sannan an ware shekaru 50 da za a riƙa biyan Bankin China a hankali kuma a kuɗin ruwa mai rahusa.
Wannan kamfani na CCCEC ya shahara a aikin madatsar ruwa, domin ko ba komai ya gina madatsar ruwa ta 3 Gorges Dam a China, wacce ita ce mafi girma a duniya cikin shekaru 12 kuma ta ninka ta Mambila sau 7.
Su Buhari sun yaudari mutane har da ɗauko Sale Mamman, ɗan Jihar Taraba, aka ba shi Ma’aikatar Lantarki, domin ana ruɗun cewa saboda ɗan Kudu ne minista a zangon farko na Buhari, shi ya sa aka ƙi yin aikin. Sale Mamman a wata hira ta BBC kafin a kore shi daga aikin ya zargi Majalisar Zartarwa ta ƙasa (FEC) a ƙarƙashin Buhari cewa, sun kasa ba shi Naira biliyan 100, domin fara aiki. Amma a ƙarshe dai yanzu sai ga Sale Mamman a hannun EFCC ta gurfanar da shi gaban kotu ana neman Naira biliyan 33 a hannunsa na aikin Mambila.
Da a ce Gwamnati Buhari ta maida hankali wajen wannan aiki daga sanda aka rattaɓa hannu a 2017, na tabbata kafin wannan shekaru bakwai lallai da CCCEC sun kammala aikin. Kuma da maganar wutar lantarki ba a Arewa ba har Najeriya da ta zama tarihi. Amma a tsawon mulkin Buhari ya sami kuɗaɗen mai da kuɗaɗen da ya karɓo bashi na jumillar Dala biliyan 312. Amma aikin aikin ƙasa da Dala biliyan 1 ya gagari Arewa. Domin kaso 15% aka nema wajensa a fara aiki har a gama, sannan daga baya a riƙa biya.
Faɗin Najeriya kaf, babu wani aiki guda ɗaya da za ka nuna a mulkin Buhari na shekaru 8 da ya kai Dala biliyan 2, a gwamnatin da ta kashe Dala biliyan 312. Kuma da a ce Mambila kawai ya yi wa Arewa da wallahi ya ceto yankin daga halin da ya ke ciki.
Don haka ’yan Arewa ku ci gaba da zama cikin duhu na zahiri na rashin wutar lantarki, da duhun talauci da jahilci da shugabanni irinsu Buhari da Sale Mamman suka haifar, ku ci gaba da abinda kuka shahara a kai na yin “Allah ya Isa”, Allah mai ji ne.
Ali Abubakar Sadiƙ manazarci ne kuma mazaunin Kano. Za a iya samun sa a imel ɗinsa na aleesadeeƙ@gmail.com