“Yanayin yadda jarumai maza da mata ke ƙoƙarin bada tarbiyya na birge ni”
Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano
Karibullahi Abdussalam Mahmud da aka fi sani da Danbaba jarumi ne a masana’artar finafinai ta Kannywood, wanda masu karatu za su fi tunawa da shi a matsayin Danbaba a fim ɗin nan mai dogon zango wato, ‘Dadinkowa’ na tashar Arewa24. A tattaunawarsa da wakilinmu a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji tarihinsa da kuma yadda ya yi finafinai fiye da 20 a ƙanƙanin lokaci. Don haka ku gyara zama, don karanta yadda tattaunawar ta kasance:
MANHAJA: Za mu so ka gabatar mana da kanka?
DANBABA: Ni dai sunana Karibullah Abdussalam Mahmud An haife ni a Unguwar ƙofar Na’isa Gwale local goɓernment. Amma na yi wayo a unguwar Fagge inda na yi primary school a fagge har ma da junior Secondary school. Sannan na tafi G.G.S.S. Zakirai burding school Kano Gabasawa local goɓernment. Daga nan naje igency of communication Gauran Dutse Kano.
Ta yaya ka samu kanka a Kannywood?
Na samu kaina a fim ta dalilin Usman Adam wanda yake da kanfanin Halidubu Moɓies Shine ya fara samun camara.
Me ya baka sha’awa ka shiga Kannywood?
Abin da yake ba ni sha’awa shi ne yadda jarumai maza da mata suke ƙoƙari wajan bada tarbiyya dadin daɗawa naga duk wanda yake sana’ar fim ba ya talauci saboda gaskiya ni da farko ma rashin aikin yi ne ya sa na shiga fim saɓanin na gama makaranta babu aikin yi.
A fim a wane ɓangare ka fi ƙwarewa?
Babu ɓangaran da ba na fitowa a fim amma an fi sanina akan shagwaba da kuma daba
Ya zuwa yanzu finafinai nawa ka yi?
Yanzu dai ina da finafinai za su fi 20 da waɗanda suka fita da kuma waɗanda ba su fita ba.
Waɗanne irin nasarori ka samu daga lokacin da ka fara zuwa yanzu?
Alhamdulillah na samu nasarori da dama a yanzu haka, waɗanda ba za su ƙirgu ba gaskiya. Alhamdulillah ta dalilin fim sunana da hotona sun je inda ma ni banje ba a rayuwa.
ƙalubale fa akwai ko babu?
Dole akwai ƙalubale da dama wani wajan idan kaje a nuna ma ƙauna kamar za a cinyeka, wani wajan kuma a kyamace ka, to ko a ‘family’ na musamman dangin babana da yake malamai ne na ci wuya kafin su fahince sana’a nake a fim.
Wane ne maigidanaka a Kannywood?
Iyayen gidan na suna da yawa gaskiya sai dai ina ji da mutum ɗaya, domin shi ne ya zama silar da aka fara sanina a duniya wananan bawan Allah bazan manta irin taimakon da yayi wa rayuwata ba, domin don badan ya koya min sana’ar fim ba da tuni ban san a wanne mataki yanzu rayuwata take ba wannan ba kowa ba ne face daraktan fim ɗin ‘Kwana Cas’in’ Salisu T Balarabe( Bozi).
Mene ne burinka a rayuwa?
Burina shi ne na gina wa mahaifiyata gida na sakata sannan ina so na samu baban jari wanda zan dinga yin ‘producing’ ɗin fim na zama oga, sannan a Kannywood ina son na sayo mota saboda ciwon ƙafata.
Baya ga fim shin akwai wani kasuwancin da kake yi ne ko babu?
Eh ina ‘online business’ inda nake saida kayan sawa na maza da na mata.
