Mata a Nijeriya sun koka da yadda ake mantawa da su bayan ’yan siyasa sun samu gwamnati duk da fitowar da suke ƙwansu da ƙwarƙwata wajen kaɗa ƙuri’a a yayin zaɓe.
Wannan koke na matan na zuwa ne a daidai lokacin da ake daf da gudanar da zaɓukan ƙasar na 2023.
Wannan matsala ta rashin damawa da mata a siyasa abu ne da ya daɗe yana ciwa wasu mata tuwo a ƙwarya ganin yadda suka ce ana watsi da su a lokacin da siyasa ta yi daɗi.
Matan na cewa wataƙila hakan baya rasa nasaba da rashin ba su cikakkiyar dama kamar takwarorinsu maza da ke mamaye fannoni daban-daban a gwamnati.
Sun kan yi ƙorafin cewa, kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu ganin yadda ake barin mata a baya.
Mata suna iya bakin ƙoƙarinsu, kuma sune ma a taƙaice ginshiƙin zaɓe, amma ana kallon abubuwa ana yi amma ba dai ga mata ba idan an ci zaɓe.
Daƙile mata ake yi ba a ba su damar fitowa a goga da su a wajen Takara.
Akwai matsalolin da matan ke fuskanta a ɓangaren siyasa na da nasaba da al’ada da kuma addini.
ƙungiyoyi da dama dai a Nijeriya na ta kiraye-kirayen a riƙa ba wa mata dama a siyasa kasancewar alƙaluma na nuna cewa su ne sama da kashi 49 cikin 100 na al’ummar Nijeriya, baya ga irin gagarumin gudunmuwar da suke bayarwa wajen zaɓen shugabanni a ƙasar.
Ina kira ga gwamnati da ta duba irin waɗanda kiraye-kiraye.
Wasiƙa daga HAJIYA AMINA FASKARI, Katsina, 08063317159 (Tes Kawai).