Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Zan fara da taya mu murna da shiga sabuwar shekarar 2025. Da fatan Ubangiji zai sada mu da dukkan alkhairan da ke cikinta, Ya kuma tsare mu daga dukkan sharrukan da ke cikinta. Allah Ya sa mu shiga wannan shekara da ƙafar dama, kamar yadda Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cikin jawabinsa na Sabuwar Shekara, wanda aka watsa ta kafafen watsa labarai, inda ya yi mana albishir da ganin sauye-sauye da kyautatuwar al’amura.
Kamar yadda ya faɗa a cikin jawabin nasa cewa, cikin shekarar 2025, Gwamnatin Tarayya za ta himmatu wajen yaƙi da tsadar rayuwa da hauhawar farashi ta hanyar haɓaka samar da abinci da masana’antun haɗa magunguna samfurin cikin gida, da sauran kayayyakin kiwon lafiya. Yayin da gwamnati ke shirin ɗaukar matakin rage hauhawar farashin kayayyaki daga kaso 34.6 cikin ɗari zuwa kashi 15 cikin ɗari.
Wannan albishir ne mai daɗi ga ‘yan Nijeriya, kuma muna fatan gwamnati za ta cika alƙawuran da ta yi mana cikin wannan shekara, don mu samu sauƙin rayuwa da bunƙasar tattalin arzili a ƙasa bakiɗaya.
Wani muhimmin abu da nake so na mayar da hankali a kansa a wannan mako shi ne yadda ’yan uwansu mu ‘yan Nijeriya, mabiya addinin Kirista suka gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara cikin kwanciyar hankali, ba tare da samun wani hargitsi ko hare-hare masu firgitarwa ba. Har kawo lokacin rubuta wannan sharhi babu wani rahoto na samun wata targaɗa a lokacin bukukuwan da aka gudanar. Wannan kuma ba ya rasa nasaba da ƙoƙarin da jami’an tsaro da gwamnati, gami da ƙungiyoyin sakai da haɗin gwiwar malaman addini, suka yi ta yi ne don tabbatar da ganin an kawo ƙarshen hare-hare da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma da ake samu duk shekara, a lokacin bukukuwa na ibada, kamar lokacin Sallah ko Kirsimeti.
Idan ba mu manta ba, tun a shekarar 2009 da aka fara fuskantar ƙalubalen tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas, sakamakon ɓullar ƙungiyar ’yan ta’addan Boko Haram, ake ta samun ƙaruwar hare-haren ta’addanci a wuraren ibada, inda ɗaruruwan rayukan masu ibada suka salwanta, cikin wani mummunan yanayi.
Maharan sun riƙa dasa bamabamai a masallatai da majami’u, da tayar da bamabamai ta hanyar ƙaunar baƙin wake.
’Yan ta’addan sun kai wani hari kan masallata da basu ji ba basu gani ba, a Babban Masallacin Juma’a na Sarki da ke Birnin Kano a ranar 27 ga watan Nuwamba na shekarar 2014, wanda ya haifar da asarar daruruwan mutane. An rawaito cewa, ‘yan ta’addan sun tayar da bamabamai uku ne a kusurwoyi daban-daban kafin daga bisani su buɗe wuta kan jama’a, suna kisan kan mai uwa da wabi.
Kafin nan ma a ranar 29 ga watan Agusta, na 2011, wasu mahara da ake zargin matasan Kirista ne sun far wa masu sallar idi a wani masallaci da ke hanyar Rukuba a cikin garin Jos, lokacin Sallar Idi ƙarama, yayin da Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, yake jagorantar sallar idin. Sakamakon wannan hari rayukan Musulmi da dama sun salwata, yayin da aka sanyawa motoci da sauran ababen hawa na masu zuwa sallar idi wuta, duk suka ƙone.
Wannan al’amarin da ya faru an yi zargin martani ne ga wani mummunan harin bom da aka kai a daren jajiberen Kirsimeti na ranar 24 ga watan Disamba, na shekarar 2010, a yankin da ake kira da Gada Biyu, inda ba shi da nisa da masallacin Idi na Hanyar Rukuba cikin garin Jos, wanda Boko Haram suka ɗauki alhakin kai harin. An yi ƙiyasin asarar rayuka kusan ɗari a daren, ban da wasu 74 da suka samu munanan raunuka. Bayan wasu tagwayen hare-hare da aka kai a wasu majami’u da ke birnin Maiduguri, a Jihar Borno.
Haka nan, idan za mu iya tunawa a ranar Kirsimeti ta shekarar 2011 wani ɗan ta’addan Boko Haram, mai suna Kabiru Sokoto ya kai hari a wata babbar majami’a da ke Madalla a Babban Birnin Tarayya Abuja. A nan ma rayukan bayin Allah da dama ne suka salwanta, yayin da rahotanni suka bayyana cewa aƙalla mutane 37 ne suka rasa rayukansu, 57 kuma suka samu munanan raunuka. Bayan harin Madalla an sake kai hare-hare a wasu majami’u da ke Jos, Damaturu da Gadaka.
A daren jajiberen Kirsimeti na shekarar 2023, an kashe mutane aƙalla 140 a wasu ƙauyuka da ke tsakanin ƙananan Hukumomin Bokkos da Barikin Ladi, wanda aka zargi Fulani makiyaya da ke ɗaukar makami da kitsa kai hare-haren.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin ɗimbin hare-haren da aka riƙa kai wa juna tsakanin Musulmi da Kirista a Nijeriya a lokutan ibada. Wani lokaci ma an fi zargin ‘yan ta’adda masu ikirarin Musulunci da kai wasu hare-haren akan ‘yan uwansu Musulmi da basu amince da ayyukan da suke yi ba. Kamar rahotannin da ke fitowa daga jihohin Zamfara, Neja, Katsina da Kaduna, inda ana tsakiyar sallah, ‘yan ta’adda ke zuwa suna buɗewa masu ibada wuta.
Amma abin da muke dubawa a yau shi ne hare-haren a wuraren ibada na mabiya addinin Kirista, a lokutan ƙarshen shekara, wanda aka shafe fiye da shekaru goma ana fuskanta.
Tsagaitawar waɗannan munanan ayyuka a shekarar da ta gabata 2024, abin farinciki ne da ya kamata a yaba wa jami’an tsaro da hukumomi, da masu faɗa a ji, saboda ba ƙaramar nasara ba ce da cigaba aka samu. Kuma lallai ne mu ɗauki darasi daga abubuwan da suka faru, a ɗauki matakan da suka dace, don kawo ƙarshensa bakiɗaya.
Kai wa juna hare-haren ramuwar gayya da kisan gilla na ba gaira ba dalili ya kamata a kawo ƙarshensa cikin wannan shekara. Masu tsokano fitina a ko ina suke a binciko su a yi maganin su, domin su ne ko da an samu daidaito da fahimtar juna, sai su je su tsokano wata damuwar da za ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyi, don kawai abin da suke kwaɗayin samu na son zuciya.
Jami’an tsaro da gwamnati su tabbatar an shawo kan matsalar ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da suke ta ƙaruwa a ƙasar nan, kama daga kan masu da’awar Jihadi, da ɓarayi masu muggan makamai kamar ‘yan bindiga da ake kira da ɓarayin daji, da ƙungiyoyin masu tada ƙayar baya da ‘yan tawaye a kudancin ƙasar nan.