Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa sheik Sani Yahaya Jingir mai cibiya a Jos ya yi kira ga al’umma musamman ma matasa akan su dage akan neman ilimi na addini dana sana’a domin zai sa a tsira daga ganganci da wauta.
Ya bayyana hakan ne a jawabinsa a lokacinda ya jagoranci buɗe Musabaƙar ƙur’ani da ƙungiyar ta shirya na jihohi sama da 20 a ƙasar nan harma da wasu daga maƙotan ƙasashe da suka shiga za a shafe tsawon kwanaki bakwai ana yi a jami’ar Bayero da ake sa ran yan takara 130 da za yi a mabanbantan izufi.
Ya yi nuni da cewa idan mutane ba suyi karatu ba za su zama ruwan tushe idan akayi duba da jihar Kano mai ƙananan hukumomi 44 amma jihar Bayalsa da ita Dattawan su a majalisa uku uku ne wato Sanata uku a Bayalsa haka ma uku a Kano don ana barci.
Sheik Yahaya Jingir ya ce sun zaɓi Kano ne domin gudanar da musabaƙar a Karo na BIyu saboda fice da tayi a sha’anin adfini irin abinda Allah ya yiwa Kano na albarka da alkhairi shekaru masu yawa da suka gabata idan aka taro mahadda Alƙur’ani tun daga Arewa mai faɗi Kanawa sun fi kowa yawan mahaddata.
Ya ce, Musulunci ya kafu a Kano don haka ƙungiyar Izala sananniyar ƙungiya ta addinin musulunci da yake jagora wacce tun daga gabatar da ƙungiyar da Marigayi Sheikh Isma’ila ya yi da shawarar babban malamin su Marigayi Sheik Mahmud Gumi a Jos shekaru 47 kenan ake ta yada addini.
Sheikh Jingir ya ce tun daga gabatar da ƙungiyar babu ranar da wa’azi ya yi baya sai daɗa gaba -gaba da taimakon Allah ƙungiya ce ta wa’azin musulunci da take dogara da hujjojin ƙu’ani da Sunnah.
Ya ce, karatun ƙur’ani alkhairan ciki Allah ne kaɗai ya san su, bayan muhimmancin karatun ƙur’ani da fahimtar sa dole sai anyi aiki dashi ba wai kasan yanda zaka karanta daidai ba kawai, babban aiki shine yin aiki da abinda yake karantar damu na shiriya.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yaba wa Gwamnatocin Kano na baya dana yanzu musamman kan hidima da take wa Ilimi ta tura ɗalibai su nemi ilimi ƙasashe daban-daban da dukkansu ya’yan talakawa ne ya jaddada kira ga matasa maza da mata su karanta ƙur’ani suyi aiki dashi.
Musabaƙar dai za a gudanar da ita ne a sassa shida izu hudu da tajewid da izu 10 tangimi da 20 da 40 da tajwidiw da izu 60 da ruwayoyi guda huɗu da tafsir da iya rubutu tambayoyi kamar yanda shugaban kwamitin musabaƙar Malam Hafiz Aminu Yusuf Nuhu.
