Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato
Haɗakar ƙungiyoyi da Hukumomin Zakka da Waƙafi ta ƙasa, (Association of Zakat and Waƙf Operators in Nigeria) mai laƙabi da AZAWON ta karrama Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato a matsayin hukumar da ta fi sauran hukumomin Zakka da Waƙafi a Nijeriya wajen ƙoƙarin karɓa da raba Zakka ga al’ummar Musulmi tare da ƙoƙarin halarta ɗaukacin tarukan da ake kira, har da ƙulla hulɗa da hukumomin Zakka na cikin ƙasa da wajen ta.
An yi wannan karramawa ce a wajen buɗe taron Zakka da Waƙafi na ƙasa karo na huɗu da ya gudana a Garin Haɗejia, inda Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa da Mai Alfarma Sarkin Musulmi ne suka gabatar da lambar girmamawa ga Shugaban Hukumar na Jihar Sakkwato, Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato.
A duk shekara ƙungiyar na karrama wasu Hukumomin Zakka da Waƙafi na Gwamnati, Masarautu da masu zaman kansu. Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa da sauran Sarkin Haɗejia da sauran manyan baƙin da suka halarci taron sun shaida bada lambar girmamawa.
Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato wacce ta soma a matsayin Kwamiti, a lokacin tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko. Sai a lokacin tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal aka mayar da ita Hukuma mai cin kashin kanta, wacce ke da damar hulɗa da sauran ƙasashen duniya.
Hukumar na da goyon bayan Gwamnatin jihar da Majalisar Sarkin Musulmi suna mara mata baya, tare da sa’ido wajen karɓar Zakka da rabonta.
Wannan ne ya ba ta damar yin zarra a tsakanin sauran hukumomin Zakka da Waƙafi na ƙasa.
