Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Kowa ya sani cewa jinin Falasɗinawa na cigaba da kwarara a Zirin Gaza musamman tun bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas. Harikan tantin da kakakin Hamas Abdel-latif ƙanoua ya ke zaune ya gamu da mummunan farmakin Isra’ila inda ƙanoua ya rasa ran sa da hakan ya shafi wasu mutane. Wani harin ma na daban a Gazan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 6 da daya kuma da a ka kashe a Khan Younis. Ba a nan Isra’ila ta tsaya ba a kashe-kashen don ta yi kisan gilla kan jigogin Hamas biyu da su ka haɗa da Ismail Barhoum da Salah Al-Bardaweel.
Jigogin nan biyu na daga mutum 20 da Isra’ila ta kashe da ke zama ginshiƙai a Hamas. Daga fara wanann yaƙin a Oktobar 2023, Isra’ila ta kashe 11 daga mutum 20 ɗin. Saboda gajiyawa da hare-haren Isra’ila da sunan murƙushe ‘yan Hamas, wasu Falasɗinawa mazauna Gaza sun yi zanga-zanga a gefen ruguzazzun gine-gine a BeitLahiya da Shijaiya su na caccakar Hamas da neman ‘yan Hamas ɗin su fice daga yankin ko a samu sararawar fitina. Masu zanga-zangar na sukar har ɓangarorin siyasar Falasɗinawa masu hamayya da juna kazalika sai Isra’ila da ke kashe mu su mata da ƙananan yara da duk wanda ajali ya sauka a kan sa. Gaskiyar magana ba a faye samun zanga-zangar ƙin jinin Hamas ba duk da a baya Hamas kan kwantar da kurar masu adawa da ita amma yanzu ta ɗan koma bayan fage tun dawo da miyagun hare-haren Isra’ila. Babban jagora a Hamas Bassem Naim ya ce jama’a na da hurumin yin zanga-zanga amma ya dace fushin ya koma kan ‘yan mamaya wato Isra’ila. A zahiri ko ma a badini za mu fahimci ɗabi’ar Isra’ila ba lallai don murƙushe Hamas kaɗai ba ne amma neman karɓe yankunan Falasɗinawa ne kakaf da mayar da jama’ar da su ka miƙa wuya tamkar bayi.
Yau ko an murƙushe Hamas ba wani sassauta hari ko cafke matasan Falasɗinawa da Isra’ila za ta yi. Kai wannan damuwar fat un 1948 ta fara yayin da a ka kwaso Yahudawa don mallake yankin Falasɗinawa. Daga 1967 komai ya wargaje ya zama Isra’ila ba wai ta raina Falasɗinawa ba ne har dukkan ƙasashen Larabawa. Duk da haka ba za a yi jam’I gaba ɗaya a ce raina Larabawa ba don akwai waɗanda a lokacin don siyasar duniya da neman haɗa kai da turai su ka yi lako-lako su ka bar Isra’ila ta yi nasara a yaƙin da a k ace ta yi da Larabawa. Har yau wadanda su ka yi wancan likimon a ka ba wa Isra’ila nasara na cigaba da tafiyar da waccar siyasar kuma za ka ga ko sun yi bayani mai zafi don kar jama’ar su su bijire ba sa samun mummunan martani daga Turai. Haba jinin Falasɗinawa ba wani abu ba ne wajen cimma muradin siyasa. Jama’a ku lura da yadda lamuran su ke gudana za ku fahimci siyasar. Mahmud Abbas da ke mulkin Falasɗinawa daga birnin Ramallah na iya nuna takaici ne kawai ga yadda a ka zubar da jinin jama’ar sa amma ba shi da kataɓus. Akwai lokacin da wani babban jami’in gwamnatin Ramallah ya ce idan an tsagaita wannan yaƙi da Hamas to ba za a ba wadan Hamas komai a mulkin yankin Falasɗinawa ba. Hadin kai ga Falasɗinawa na da muhimmancin gaske matuƙar za su iya ceto ‘yancin ƙasar su daga ‘yan mulkin mamaya. Duk wani taimako ko nuna goyon baya daga wata ƙasa ba zai yi tasirin da a ke buƙata ba matuƙar Falasdinawa ko ɓangarorin siyasar su na rayuwa cikin rabuwar kai.
Isra’ila ta kashe fiye da Falasɗinawa 50,000 a yaƙin da ta ke cigaba da yi kan al’ummar Gaza da ya fara daga Oktobar 2023.
Ma’aikatar lafiyar Zirin Gaza ta ba da labarin adadin mutanen da Isra’ila ta kashe sun ƙaru bayan wani harin dare ɗaya na ruwan boma-boman Isra’ila da ya kashe Falasɗinawa 26 ciki da mata da ƙananan yara.
Isra’ila dai ta yanke yarjejeniyar tsagaita wuta makon jiya inda ta takarkare da hare-hare ta sama da ma tura sojojin kasa zuwa garin Rafah na kudancin Gaza.
Kazalika fadar Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ta kafa wata cibiya da za ta kula da kaurar Falasɗinawa ta kashin kai daga Gaza don cimma burin muradin shugaban Amurka Donald Trump na kaurar da Falasɗinawa daga Zirin da sunan sake gina shi.
Haƙiƙa Falasdinawa sun yi watsi da neman kaurar da su da zaiyana hakan da maƙarƙashiyar raba su da ƙasar su ta gado.
Za a jira a ga martanin da ƙasashen Larabawa za su yi kan ruwan wutan na Isra’ila tun da su ma sun fito ƙarara sun yi watsi da neman kaurar da al’ummar Gaza.
Hakanan za a saurari bayanan da za su fito daga Masar da Katar da ke jagorantar sulhun tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.
Ita dai Isra’ila na nuna ta na yaƙi da don ƙarar da Hamas da bayyana cewa sabon harin ta ya hallaka gomman ‘yan Hamas da ta ke zaiyanawa da tsagera.
ƙasar Saudiyya ta yi Allah wadai da hukumar da Isra’ila ta kafa da zummar kaurar da Falasɗinawa daga yankin Gaza zuwa wasu ƙasashe 3 da ba a tantance ba.
Ma’aikatar wajen Saudiyya ta yi tir da wannan mataki na Isra’ila bayan majalisar Knesset ta amince da kafa hukumar wacce za ta lura da kaurar da al’ummar Gaza daga mahaifar su.
Hakanan Saudiyya ta kara Allah wadai da yanda Isra’ila ta amince da mallake yankunan share-waje-zauna na al’ummar ta a yankunan Falasɗinawa na yammacin gabar tekun Jodan.
Saudiyya ta ce ware matsugunai 13 a yankin yammacin Kogin na Jodan na nuna niyyar Isra’ila ta mulkin mallaka da babakere a yankin da ba na ta ba.
Wannan inji Saudiyya karantsaye ne da Isra’ila ke yi ga dokokin duniya.
A nan Saudiyya ta ce hanyar maslaha ita ce a tabbatar da kafa ƙasar Falasɗinawa a gefe da Isra’ila bisa kan iyakokin da a ka shata gabanin shekara ta 1967 da gabashin birnin ƙudus a matsayin babban birnin kƙasar Falasɗinu.
A gefe guda ga ƙungiyar Houthi da ke marawa gwagwarmayar Hamas baya, Amurka na binciken yanda bayanan sirri na yanda ta ke shirin hare-hare kan ƙungiyar Houthi a Yaman su ka faɗa komar babban editan kafar labarun ATLANTIC.
Manyan jami’an gwamnatin Trump sun bayyana samun kuskuren da ya sa ‘yan majalisar dokoki na Dimokrats caccakar sakacin da baiyana aniyar ƙaddamar da bincike.
Editan Jeffrey Godlberg ya ce ya samu gayyata ga dandalin musayar bayanan sirrin kan duk tsari da inda Amurka za ta kai hare-hare kan Houthi.
Goldberg ya lissafa manyan jami’an gwamnatin Trump da musamman masu hannu kan lamuran tsaro na cikin dandalin.
Da a ka tambayi Trump kan akasin; ya ce ba ya bin labarun Atlantic don haka bai san abun da ya wakana ba.
Daga bisani an yi wa Trump cikekken bayanin lamarin kuma an tabbatar za a ƙaddamar da binciken yadda bayanan su ka shiga hannun ɗan jaridar.
ƙungiyar mayaƙan Houthi a Yaman ta ba da labarin cigaba da hare-haren Amurka kan yankunan ƙasar ta Yaman da hakan ya shafi jama’a.
Sabon harin dai kamar yanda Houthi ta wallafa a kafar labarun ta, ya shafi yankin Saada da Amran ne.
In za a tuna shugaban Amurka Donald Trump ya lashi takobin gamawa da Houthi don kawo ƙarshen barazana ga jiragen dakon man Amurka da ƙawayen ta a Bahar Maliya da mashigar tekun Aden.
Tun fara miyagun hare-haren da jiragen yaƙi, Amurka ta yi sanadiyyar kisa ga mutum 53 kuma daga nan hare-haren kusan kullum na aukuwa a sassan da Houthi ke jagoranta.
Houthi dai da Iran ke marawa baya ta nanata ba za ta ja da baya wajen kai hare-hare kan muradun ƙasashen da ke mara baya ga Isra’ila a yaƙin Gaza ba.
Kammalawa;
Duk inda Isra’ila ta huda ta ga jini sai ta cigaba da yin gaban kan ta da fakewa da cewa ta na kare kan ta ne daga maƙiya. Isra’ila ta cigaba da kai hare-hare a kudancin ƙasar Sham duk da ba wata barazana da ta ke fuskanta daga Sham ɗin.
Gabanin kawar da mulkin tsohon shugaba Bashar Al’Asad, Isra’ila ta shafe shekaru ta na kai hare-hare da sunan karya lagon mayaƙan da Iran ke marawa baya da tare hanyar tura makamai ga ’yan Hezbollah a Lebanon.
Sabon harin ta jirgin yaƙi ya yi sanadiyyar kisan gilla ga mutum 6 inda Isra’ila ke cewa ba za ta lamunci ’yan bindiga su zauna a kan iyakar ba duk da ƙasar ta ba ne.
Sabbin shugabannin Sham a birnin Damaskas na Allah wadai da cigaba da hare-haren da buƙatar duniya ta shiga tsakani don ba ta sha’awar yaƙi kai tsaye da Isra’ila.
ƙungiyar taraiyar Turai ta yi kira ga Isra’ila ta daina kai hare-haren don gaskiyar magana ba ta fuskantar barazana daga yankin.
A ganawa da ministan wajen Isra’ila Gideon Saar, sakataren tsare-tsare na ƙungiyar Kaja Kallas ya ce baa bun da hare-haren za su haifar sai fadada fitina.
ƙungiyar ta tarayyar turai ta ba wa shugabannin Sham shawarar sam kar su yarda da muzgunawa ko kawo mu su wani cikas na lakace hanci.
