Edo: ‘Yan binga sun sace shugaban IPMAN, sun halaka direbansa

‘Yan bindiga a jihar Edo sun sace shugaban Ƙungiyar Dillalan Fetur ta Ƙasa (IPMAN) reshen Jihar Edo, Abdullahi Baba-Saliu, kana suka harbe ɗaya daga cikin direbobinsa da bindiga har lahira.

‘Yan bindigar sun kai harin ne gidan Baba-Saliu da ke Jattu, cikin ƙaramar hukumar Etsako ta Yamma a jihar, inda suka kutsa sannan suka aikata aika-aikarsu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Bello Kotongs, ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da cewa, suna kan ƙoƙarin ceto wanda aka yi garkuwar da shi.

Bayanan ‘yan sanda sun nuna yayin harin, an jikkata masu tsaron wanda aka sace da kuma ɗayan direbansa. Rahotanni daga jihar sun ce lamarin ya faru ne da yammacin jiya Litinin.

Wata majiya ta kusa da wanda lamarin ya shafa ta ce har yanzu ‘yan bindigar ba su tuntuɓi iyalansa ba.

A cewar majiyar, “A daren jiya misalin ƙare 6:45 na yamma, ‘yan bindiga sun sace surukina, Abdulhamid Baba-Saliu, bayan sun kutsa gidansa a garinsu Jattu da ke ƙaramar hukumar Esako ta Yamma.

“Yana zama ne a Benin, Abuja da Jattu inda yake da gidajen man fetur. Ya tafi gida ne domin halartar addu’ar ranar uku na rasuwar kawunsa a makon da ya gabata.

“An kashe ɗaya daga cikin direbobinsa bayan harbinsa da aka yi da bindiga; ɗayan direban da kuma masu tsaronsa duk sun samu munanan raunuka. Masu garkuwa da mutanen sun tafi da surukina. Ba su tuntuɓi kowa ba, ba su nemi kuɗin fansa ba a yanzu.”

Majiyar ta ci gaba da cewa, “Yanzu muna cikin mawuyacin hali, yayin da muke ci gaba da addu’a da roƙon waɗanda suka sace shi da su sake shi ya dawo cikin ahalinsa da mutanensa…”