EFCC ’yar amshin Shata ce!

Hukumar Hana Cin Hanci da Karɓar Rashawa (EFCC), muna jin irin yadda ki ke ƙoƙari wajen gano masu wawure dukiyar ƙasa inda suke azurta kansu suna ƙoƙarin nakasa ƙasarmu.

Duk da dai ji ne muke yi kin gano wane kowane ko suwane sun yi handama da baba-kere ko yin awon gaba da dukiyar ƙasa! Na sha ganin wasu maka-makan gidaje ko wasu gine-gine da hukamar EFCC ta kama inda har ta ke rubuta sunanta ajikin gidajen ko gine-ginen.

Hakazalika, muna jin yadda hukumar ke cewa ta amso ko ta kwato maƙudan kuɗaɗen da wasu marasa kishin ƙasa suka handame.

Sai dai ba kasafai bane mukejin yadda hukumar ke ƙarewa da masu halin veran ba! Shin abin tambayata anan wannan vavatu ko in ce cika baki ko bugun ƙirji da hukumar ke yi akan yadda ta gano masu yi wa ƙasarmu ta’annati.

Shin hakan ya kawo qarshen masu aikata laifin ne? Koko laifin ya yi sauƙi sosai? Shin me ya sa mu jama’a sai dai mu ji farkon labari amma bama jin qarshensa? Tambayar jama’a da dama me ya sa hukumar ba ta bayyana wa jama’a yadda ta ƙare da masu halin verayen?

Kuma ina ake yi da maƙudan kuɗaɗen da maka-makan gine-gine da danƙara-danƙaran motoci ko sauran ababen hawa da ake cewa an ƙwato?

Rashin samun ƙarashen labarin daga wannan hukuma ne ya sa wasu jama’a ke cewa, “Ko dai ja ne yake faɗowa ja yana ɗaukewa?”

Hujjar da masu wannan magane ke badawa shi ne. Idon har da gaskene wannan Hukuma tana kwato kuɗaɗen yaka mata arinƙa gani a ƙasa ta hanyar yima jama’a ayyukan raya ƙasa waɗanda zasu inganta rayuwar su.

Duba da ganin kusan kullum ana cewa an ƙwato Naira kaza ko milyan kaza ko tiriliyan kaza ko kuma dala ko Yuro ko fam kaza. Kuma kullum cewa ake yi babu kuɗin da za aima jama’a aikin ci gaba!

Saboda haka idon har waɗannan hukuma da gaske take yi tana kwato maƙudan kuɗeɗen da gine-gine daga hannun masu yunƙurin karya ƙasarmu to yakamata ta rqa fitowa a kafafen yaɗa labari Jaridu/Gidajen Rediyo/Talabijin da hanyoyin sada zumunta na zamani da duk wasu hanyoyin isar da saƙo su gaya wa jama’a gaskiyar abin da ke faruwa da inda kuɗaɗen suka bi, gami da abubuwan da aka yi da kuɗin domin yin hakan ne zai fitar da hukumar daga zargin da ake yawan yi mata.

A ƙarshe ina yin kira ga hukumar da ta ƙara azama sosai wajen ganin ta tallafawa sabon Shugaban Ƙasa da sababin Gwamnoni dama sauran duk wasu masu riƙe da muƙamai musamman ganin mafi yawan su suna cewa, “magabatansu wato waɗanda suka gada sun yi wawaso da dukiyar ƙasa/jihq ko yankin su”!

Kai akwai wani gwamna ma da ya sha kaye ake zarginsa kafin yabar gidan Gwamnatin ya yi awon gaba da wasu kayayyakin Gwamnati hatta akwatunan talabijin da kayan kicin da ake yin sanwa da su da injunan bayar da hasken wutar da gadaje da na’urorin sanyaya ɗaki duk ya kwashe! Akwai wasu tsaffin gwamnonin bayan sun tarrwatsa arzikin jihar a larshe suka yima kansu da mataimakansu da kwamishinoni sallamar data wuce kima!

Saboda haka nike kira ga Hukumar EFCC ta haska fitilarta ko taje da jiƙaƙƙun igiyoyinta masu kauri jihohin da ake zargin hakan ya faru domin ta kamo ɓerayen gami da kwato duk abinda suka sace akuma maido dukiyar ga jihohin sannan a kuma sanya ido ga jagororin jihar na ganin sun yi aiki da dukiyar a inda ya dace.

Haka shima Shugaban Ƙasa Ahmed Bola Tinubu ya kamata hukumar da ta tallafa masa wajen gano masu sata da suka lacce dukiyar ƙasa! Duba da ganin gwamnatin da ta gabata ta Buhari ta ciyoma ƙasarmu ɗimbin basukan da har sun kai iya wuya ga ɗimbin harajin da aka sanya wa kamfanoni da Masana’antu gami da ƙanananan ’yan kasuwa, wanda hakan ya sa kayayyaki su ka yi mummunan tashi inda jama’a ke ɗanɗana kuɗarsu kafin su samu su sayi koda magin miya ne ko garin kwaki da dai sauran su.

Kuma duk da irin wannan haraji da gwamnatin ke amsa ga kuma ɗumbin bashin da ta jibgoma ƙasar zan iya cewa tunda aka ƙirƙiro wannan ƙasa ba a tava samun maƙudan kuɗaɗe ba kamar a gwamnatin Buhari.

Hakazalika, jama’a ba su tava shiga cikin mummunan ƙunci da tsadar rayuwa mai muni ba sai a gwamnatin Buhari!

Bugu da ƙari, sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gaji wasu ɗimbin basuka gami da gadar wasu manyan ayyukan da ba a kammala ba kuma kamfanonin suna bin tiriliyoyin Naira wadda kuma Gwamnatin Bola ɗin ce za ta biya shi.

Saboda haka nike yin kirada babbar murya ga EFCC da ta taimaki wannan sabuwar Gwamnatin wajen ganowa gida hukunta duk wanda ya sace dukiyar ƙasa a zaman Gwamnatin Buhari da kuma a cikin wannan Gwamnatin kuma yima Jama’a ayyukan cigaba.

Duba da ganin har yanzu jama’a basu dawo cikin hayyacinsu ba daga halin ƙunci da tsadar rayuwa wanda Gwamnatin Buhari ta jefesu a ciki!

Yin hakan zai saka jama’a su yi amannan da hukumar sannan su daina yi mata kallo tamkar ‘yar amshin Shata ce, wato mai bin umurnin wani ko wasu inda ta zama tamkar karen farauta ce. Inda wasu ko wani ke ingizata ta ci mutuncin wani ko wasu ko suna yin zaman doya da manja ko suna yin kallon hadarin kaji da iyayen gidan hukumar.

Daga Haruna Muhammad, Katsina. Shugaban Ƙungiyar MURYAR JAMA’A. 07039205659 ko 08121355933.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *